Okupe: Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Ya Fice Daga Jam'iyyarsa, Ya Bayyana Muhimmin Dalili
- Mista Doyin Okupe, tsohon kakakin shugaban ƙasa sau biyu, ya fice daga jam'iyyar LP ranar Litinin, 8 ga watan Janairu
- Tsohon darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaben Peter Obi ya ce ba zai iya ci gaba da zama a LP ba bayan sun sha kaye a 2023
- Okupe, ya sha fama da shari'a kan halatta kuɗin haram wanda ya jawo babban koma baya a kamfen Obi/Datti
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Doyin Okupe, ya fice daga jam'iyyar LP.
Mista Okupe, tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa ya tabbatar da sauya sheƙa daga LP ne a wata sanarwa da ya aike wa jaridar Vanguard ranar Litinin.
A sanarwan, Okupe ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina miƙa takardata ta fita daga LP daga yau. idan baku manta ba Peter Obi da ni mun bar jam'iyyar PDP kwatsam domin neman inuwar da zamu shiga takarar shugaban ƙasa a 2023.
"Jam'iyyar LP da shugabanninta gaba ɗaya sun samar mana da wannan inuwa kuma muna ƙara gode muku bisa karamci. Mun tsaya takara amma mun sha kaye.
"Wannan ya sa ba zan iya ci gaba da zama a jam'iyyar Labour Party ba. Ina mika godiya ta musamman gare ku da sauran shugabanni bisa irin karramawa da aka yi mini a matsayin Darakta Janar na kamfen Obi-Datti."
Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a baya
Idan baku manta ba, Mista Okupe ya janye daga kwamitin kamfen Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP a 2023, cewar rahoton The Cable.
Okupe, ƙwararre ne kuma gogaggen ɗan siyasa wanda ya riƙe mai magana da yawun taron jamhuriya ta uku wanda aka yi a farkon shekarar 1990.
Haka nan kuma ya yi mai magana da yawun shugaban kasa sau biyu, inda ya yi aiki da tsoffin shugabannin ƙasa 2, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Hukuncin da kotu ta yanke na kama Okupe da hannu a halatta kuɗin haram ya jawo naƙasu ga yakin neman zaben Obi.
Tinubu Ya Dakatar da Ministar Harkokin Jin Kai
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Dokta Betta Edu daga matsayin ministar harkokin jin kai da yaƙi da talauci kan badaƙalar kuɗi.
Shugaban ƙasar ya kuma umarci hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan zargiin da ake wa ministar da wata hukuma.
Asali: Legit.ng