Kano: Ana Daf da Yanke Hukuncin Zabe, Abba Kabir Ya Samu Karfin Gwiwa Daga Majalisar Jihar
- Ana daf da yanke hukuncin zaben jihar Kano, Majalisar jihar ta yi addu'a na musamman ga Gwamna Abba Kabir
- Majalisar ta yi wannan addu'a ce yayin taya Gwamna Abba Kabir bikin cika shekaru 61 a duniya
- Kakakin Majalisar, Hon. Isma'il Jibril Falgore a madadin Majalisar gaba daya ya bayyana gwamnan a matsayin mai cika alkawari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Majalisar jihar Kano ta yi addu'a na musamman yayin da ake dakon shari'ar zaben gwamnan jihar.
Majalisar ta yi wannan addu'a ce yayin taya Gwamna Abba Kabir bikin cika shekaru 61 a duniya.
Mene Majalisar ke cewa kan Abba Kabir?
Kakakin Majalisar, Hon. Isma'il Jibril Falgore a madadin Majalisar gaba daya ya bayyana gwamnan a matsayin mai cika alkawari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Falgore ya ce gwamnan ya fifita bukatun al'umma da ci gaban jihar Kano a kan dukkan bukatunsa na karan kai.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Majalisar jihar, Uba Abdulllahi ya fitar.
Sanarwar ta ce mutanen jihar Kano shaida ne kan irin abubuwan more rayuwa a jihar ta bangarori da dama, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Wane roko Majalisar ta yi ga 'yan Kano?
Hon. Falgore ya bukaci 'yan jihar Kano da su goyi bayan gwamnatin jihar a kokarinta na inganta rayuwar al'ummar Kano.
Ya kuma yi addu'ar samun nasara ga Gwamna Abba Kabir yayin ake dakon hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar.
A karshe, ya yi addu'ar Allah ya bai wa gwamnan tsawon rai masu albarka don ci gaba da ayyukan alkairi a jihar, cewar PM News.
'Yan sanda sun yi ganawa da 'yan daba 52
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta yi zama na musamman da 'yan daba 52 a jihar Kano.
'Yan daban sun fito ne daga yankin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru don samun zaman lafiya a jihar.
Wannan na zuwa ne yayin ake dakon hukuncin Kotun Koli bayan ta tanadi hukunci a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng