Na Kusa da Gwamnan PDP Ya Ɗauki Matakin Ƙarshe Kan Yan Majalisa 25 da Suka Koma APC
- Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ribas ya janye karar da ya shigar da yan majalisa 25 da suka sauya sheka zuwa APC
- Edison Ehie, mai biyayya ga Gwamna Fubara ya janye karar ne a wani ɓangare na yarjejeniyar sulhu da aka cimma a Villa
- Ana ganin dai wannan wata babbar alama ce da ke nuna karshen rikicin siyasar da aka jima ana yi a jihar Ribas mai arzikin man fetur
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Tsohon mamban majalisar dokokin jihar Ribas, Edison Ehie, ya janye ƙarar da ya shigar da ƴan majalisa 25 cikin 27 da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Mista Ehie, wanda ya wakilci mazaɓar Ahoada ta gabas II, ya janye ƙarar da ya maka ƴan majalisar dokokin jihar 25 bisa zargin raini, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ga dukkan alama matakin Ehie na janye ƙarar ya kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da dambarwan siyasar da suka mamaye jihar mai arzikin man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rikicin ya samo asali
Ehie, wanda ya yi ikirarin zama shugaban majalisar ya ayyana kujerun mambobin guda 27 a matsayin waɗanda babu kowa a watan Disamba, 2023.
Ya yi haka ne a wancan lokacin sakamakon sauya sheƙar da suka yi daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.
Sai dai daga baya biyu daga cikin ‘yan majalisar sun lashe amansu, suka sake komawa jam’iyyar PDP.
Haka kuma tawagar mambobi 5 da ke goyon bayan Gwamna Fubara, Ehie ya jagorance su a wancan lokacin, kamar yadda Channels tv ta tattaro.
A daya bangaren kuma Gwamna Fubara ya sha fama da rikicin siyasa mai zafi tsakaninsa da magabacinsa, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja.
A baya, Ehie ya shigar da kara gaban babbar kotun jihar Ribas da ke Fatakwal, inda ya kalubalanci taron da ƴan majalisa 25 suka yi da kuma matakin da suka dauka a zaman.
Sai dai kuma a wani juyin yanayi, Ehie ya yi murabus daga Majalisar lokacin da Gwamna Fubara da Wike suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya.
Ganduje Ya Kara Yi Wa Jam'iyyar PDP Lahani
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta kara haifar da babban giɓi mai wuyar cikewa a jam'iyyar PDP reshen jihar Benuwai.
Wasu manyan jiga-jigai da shugabanni akalla 9 suka jefar da tafiyar PDP, kana suka sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.
Asali: Legit.ng