Dan Takarar Gwamna Kuma Sanata Ya Watsar da Jam’iyyarsa Zuwa APC, Ya Bayyana Manyan Dalilai
- A karshe, dan takarar gwamna a jihar Rivers, Magnus Abe ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Abe ya yi takara ne a jam’iyyar SDP a zaben da aka gudanar a watan Maris wanda tun asali dan jam’iyyar APC
- Alamu sun nuna Abe tuntuni ya shirya koma wa jam’iyyar ta APC mai mulkin kasar a wata hira da ya yi da ‘yan jaridu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers – Dan takarar gwamnan jihar Rivers a jam’iyyar SDP, Magnus Abe ya sauya sheka zuwa APC.
Abe ya yi takara a zaben da aka gudanar a watan Maris da ta gabata inda ya ce ya dawo APC ne saboda ayyukan alkairi na Shugaba Tinubu.
Yaushe Abe ya nuna alamun sauya shekar zuwa APC?
A ranar Litinin da ta gabata Abe ya nuna alamun koma wa jam’iyyar APC yayin hira da gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.
Yayin hirar Abe ya ce:
“A siyasance ina kan koma wa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.”
Mene martanin dan takarar gwamnan?
Tsohon sanatan ya yi alkwarin jawo dukkan dubban magoya bayansa zuwa jam’iyyar ta APC, cewar The Nation.
Abe ya sauya sheka zuwa APC ne ana daf da gudanar da zaben shekarar 2023 zuwa SDP
Komawarsa jami'yyar SDP ke da wuya ya samu tikitin zaben gwamnan jihar da aka gudanar.
Yayin da ya ke jawabi a birnin Port Harcourt a yau Laraba 3 ga watan Janairu, Abe ya ce ya koma tsohuwar jami'yyarsa ce saboda ayyukan alkalin Tinubu.
Magnus Abe ka iya sauya sheka zuwa APC
A wani labarin, dan takarar gwamnan jihar Rivers a jami'yyar SDP ka iya koma wa APC.
Magnus Abe wanda ya yi takara a zaben watan Maris da ta gabata ya bayyana alamu a wata hira da manema labarai.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng