Kotun Koli Na Shirin Yanke Hukunci, Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sake Motsi Mai Girma a Jihar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shaida bikin rantsar da manyan sakatarori 11 tare da sabbin masu bada shawara ta musamman 14
- Ya yi wannan ne yayin da ake ci gaba da dakon zaman karshe na yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano a kotun koli
- Abba ya roƙi waɗanda ya naɗa da su guji amfani da siyasa wajen ayyukan da aka ɗora musu, yana mai ba su shawara da su yi don Allah
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin guda 21 ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2023.
Bayan rantsar da manyan sakatarorin, Gwamna Abba ya kuma shaida rantsuwar kama aiki na sabbin masu ba shi shawara ta musamman guda 14, kamar yadda Channels tv ta tattaro.
Abin da Gwamma Abba ya gaya wa sabbin hadiman
Da yake jawabi a wurin bikin rantsarwan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa bai nuna banbancin siyasa ba wajen naɗa mutanen kuma an zaƙulo su ta hanya mai tsafta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci sabbin hadiman da aka nada da su yi kokari wajen ganin sun yi aiki tukuru da yi wa al'umma hidima.
Gwamna Abba ya ƙara musu kwarin guiwa da cewa gudummawar da suke bayarwa na da muhimmanci wajen gina kyakkyawar makoma ga jihar Kano.
Haka zalika, ya roki wadanda aka nada da su sadaukar da kansu da zuciya daya wajen yi wa jama’a hidima da kuma ciyar da kasa gaba.
A cewarsa, gwamnatinsa na nan a kan bakarta na cewa ba zata lamurci rashin kwazo da rashin iya aiki daga kowane mutum da ta bai wa dama a gwamnati ba.
Ya ce:
"Duk da na san ɗan adam tara yake bai cika goma ba amma ina rokon ku yi taka tsan-tsan kuma ku iya iya iyawarku wajen cika rantsuwar da kuka yi."
Gwamnan ya kuma shawarce su da su guji amfani da siyasa a matsayin ma’auni wajen gudanar da ayyukansu, inda ya buƙaci su sa ikhlasi da guje wa tsegumi.
Filato: Makomar APC da PDP a kotun koli
A wani rahoton kuma Malami ya buƙaci Gwamna Celeb Mutfwang ya dage da addu'a ba don ya tsira da kujerarsa kaɗai ba harda neman kariya daga hare-hare.
Joshua Iginla, wanda ya yi hasashen kan makomai gwamnan Filato a kotun koli, ya ce ya hangi wani mutum daban ya kwace kujerarsa.
Asali: Legit.ng