Tinubu Ya Jawo ‘Yan Najeriya Sun Ci Kwa-Kwa a 2023, A Saurari 2024 In Ji Gwamnan PDP

Tinubu Ya Jawo ‘Yan Najeriya Sun Ci Kwa-Kwa a 2023, A Saurari 2024 In Ji Gwamnan PDP

  • Mai girma Gwamnan jihar Enugu ya ce al’umma sun galabaita a sakamakon tsare-tsaren Bola Ahmed Tinubu
  • Peter Mbah ya ce dole gwamnatin tarayya ta dauki matakin janye tallafin man fetur da daidaita kudin kasan waje
  • Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawari za a samu cigaba ta fuskar tattalin arziki a sabuwar shekarar nan ta 2024

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce yana mai sa rai wahalar da ake sha a Najeriya za ta kare a shekarar 2024.

Gwamna Peter Mbah ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi jawabin shiga sabuwar shekara, The Cable fitar da rahoton.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Peter Mbah Hoto: @AjuriNgelale da @PNMbah
Asali: Twitter

Mai girma gwamnan ya yi wa al’ummar Najeriya da na jihar Enugu jawabi a ranar Lahadi ganin za a shiga shekarar nan.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Abu 1 da Ba Zai Yi Tasiri ba a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mbah ya wanke Tinubu

Mbah yake cewa mutane sun sha wahala sosai saboda tsare-tsaren da su ka zama dole da gwamnatin tarayya ta fito da su.

"Shakka babu shekarar 2023 ta yi wa ‘yan Najeriya wahala, musaman wahalar da aka shiga saboda wasu tsare-tsaren gwamnatin tarayya masu wahala da su ka zama dole, irinsu cire tallafin fetur da daidaita kudin kasashen waje.
Amma ina da yakinin cewa hauhawar farashi, rashin aikin yi da yawan tsadar rayuwa zai ragu a shekarar da za a shiga (2024).”

- Peter Mbah

"Dadin yana gaba" - Gwamna Mbah

Rahoton ya ce gwamnan ya yi kira ga mutanen jiharsa ta Enugu su cigaba da sa rai, ya kara da cewa za a samu cigaban tattalin arziki.

Gwamnan ya ci burin ganin jihar Enugu ta zama wurin zuwan ‘yan kasuwa da ‘yan yawon shakatawa ta yadda za a samu kudin shiga.

Kara karanta wannan

2024: Shugaba Tinubu ya bayyana babban buri ɗaya tal da ya sa ya nemi hawa mulki sau 3 a Najeriya

...Tinubu zai kawo cigaba a 2024

Shi kuwa Bola Ahmed Tinubu ya yi hasashen ya ce tsare-tsarensa za su kawo cigaban tattalin arziki a sabuwar shekarar nan ta 2024.

Tribune ta rahoto shugaban kasar ya yi wannan magana ta bakin Temitope Ajayi a Ekiti.

Da yake jawabi wajen taron kungiyar tsofaffin ‘yan makarantarsu, Ajayi ya ce shugaba Bola Tinubu ya san halin da jama’a su ke ciki.

Majalisar tarayya a shekarar 2023

A majalisar dattawa da wakilan tarayya, kun ji labarin yada tun daga zabe aka zazzage fitattun ‘yan siyasa da ake ji da su a kasar nan.

Da aka yi zabe, sai aka fara fafutukar wadanda za su jagoranci ‘yan majalisar daga jam’iyyar APC, daga nan aka koma rikicin kasafin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng