Ganduje Ya Yunƙuro, Jam'iyyar APC Ta Fara Shirin Ƙwace Mulki Daga Hannun Wani Gwamnan PDP
- Jam'iyyar APC ta ayyana shirin da take na karɓe ragamar mulkin jihar Ribas daga hannun jam'iyyar PDP a babban zaben 2027
- Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta jihar, Chief Tony Okocha ne ya faɗi haka a Fatakwal, babban birnin jihar
- Kodinetan kungiyar tsoffin shugabannin ƙananan hukumomin APC ya ce za su ba kwamitin goyon baya da haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Shugaban kwamitin riƙon kwarya na jam'iyyar APC ta jihar Ribas, Chief Tony Okocha, ya bayyana shirin da jam'iyyar ke yi na tunkarar zaben 2027.
Mista Okocha ya bayyana cewa shugabannin APC sun kudiri aniyar kwace gidan gwamnatin jihar Ribas idan Allah ya kaimu zaɓe na gaba, Leadership ta ruwaito.
Okocha ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da kungiyar tsaffin shugabannin kananan hukumomin APC, suka kai masa ziyara ta musamman a gidansa dake Fatakwal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC ya sake tabbatar da cewa jam’iyyar a karkashin shugabancinsa, za ta gudanar da mulki na bai-daya.
Zamu baku goyon baya - Aribodor
Tun da farko a nasa jawabin, kodinetan ƙungiyar, Hon Frank Aribodor, ya ce sun yanke shawarar ziyartar Okocha ne domin tabbatar masa da mubaya'ar su.
Ya kuma ƙara da cewa kungiyar tsofaffin ciyamomin zasu bai wa Okocha da sauran jagororin APC na jihar Ribas goyon baya, da kuma cikakkiyar biyayya a gare su.
Mista Aribodor ya kuma jaddadabwa shugaban jam'iyyar cewa kungiyarsu a shirye take ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da kwamitin rikon kwarya wajen farfaɗo da APC gabanin zabe na gaba.
Ya yabawa Okocha bisa bajintar sa na shugabanci, wanda tuni ya samar da gagarumin sakamako ga jam’iyyar APC na jihar Ribas, Guardian ta tattaro.
Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin kudin 2024
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2024 ya zama doka daga yau Litinin, 1 ga watan Janairu.
Shugaban ƙasan ya dira ofishinsa da misalin karfe 2:00 na rana kuma kai tsaye ya wuce ɗakin bikin sa hannu kan kasafin.
Asali: Legit.ng