Kano: Dan Majalisar NNPP Ya Sha Suka Bayan Kaddamar da Shiri Da ’Yan Mazabar Suka Bayyana Abin Kunya

Kano: Dan Majalisar NNPP Ya Sha Suka Bayan Kaddamar da Shiri Da ’Yan Mazabar Suka Bayyana Abin Kunya

  • Dan Majalisar Tarayya a jihar Kano ya sha suka bayan kaddamar da wani shiri na yi wa yara fiye da dubu daya a mazabarsa kaciya
  • Mohammed Bello Shehu wanda ke wakiltar mazabar Fagge a Majalisar Wakilai ya kaddamar da shirin ne a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba
  • ‘Yan siyasa sun soki shirin na dan Majalisar inda suka bayyana hakan a matsayin abin kunya a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Fagge a jihar Kano, Mohammed Bello Shehu ya sha suka kan kaddamar da wani aiki.

Dan Majalisar ya kaddamar da yin kaciyar yara fiye da dubu daya a unguwanni 11 da ke mazabarsa, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi matsala 1 da ta wajaba Shugaba Tinubu ya shawo kan ta a shekarar 2024

Dan Majalisar Kano ya sha suka bayan kaddamar da shirin kaciya
MB Shehu ya sha bayan kaddamar shirin shirin kaciyar yara a mazabarsa. Hoto: MB Shehu.
Asali: Facebook

Mene dan Majalisar ya kaddamar?

Kaciya dai wata al’ada ce da al’ummar Hausawa ke yi a lokacin hunturu ga yara kanana don kare su daga cututtuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu an zabe shi ne a karkashin jam’iyyar NNPP a Kano wanda ya kaddamar da aikin a ranar Lahadi 31 ga watan Disamba.

Sai dai wannan shiri na dan Majalisar ya sha suka daga ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki inda suka ce wannan abin kunya ne.

Har ila yau, magoya bayansa sun koka ganin yadda ya samu nasara a Kotun Daukaka Kara a kwanakin baya, Media Talk Africa ta tattaro.

Wane martani 'yan mazabar ke yi?

Sun koka ko dan Majalisar zai iya cika alkawuran da ya dauka wa ‘yan mazabarsa da suka zabe shi a watan Faburairu.

Daya daga cikin magoya bayan dan Majalisar, Ibrahim Usaini ya bayyana rashin jin dadinsa inda ya ce wannan abin kunya ne.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fusata kan tsaro, ya tura zazzafan gargadi ga sabbin sojin da suka samu karin girma

Ya ce hakan bai dace ba ganin yadda abin ya zo yayin da ‘yan mazabar ke cikin mawuyacin hali bayan cire tallafin mai a kasar.

Ya kara da cewa madadin ya raba wa mutane kayan rage radadi amma ya bige da kaciyar yara wanda hakan bai zama dole ba.

Wani jigon NNPP, Basiru Chile ya shawarci dan Majalisar da ya duba halin da ake ciki a mazabar don rage musu radadi.

APC ta yi magana kan shari’ar zaben Kano

A wani labarin, Jam’iyyar APC a jihar Kano ta bayyana kwarin gwiwar yin nasara a shari’ar zaben jihar Kano.

Wannan na zuwa ne yayin da aka tanadi hukunci a Kotun Koli inda a yanzu ake dakon hukuncin kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.