Talakawa Na Kukan Na Abinci, an Warewa Majalisa Biliyoyin Don Siyan Littafai

Talakawa Na Kukan Na Abinci, an Warewa Majalisa Biliyoyin Don Siyan Littafai

  • Gwamnatin Najeriya ta daddale kan kasafin kudin shekarar 2024, majalisa ta amince tare da yin kari a kai
  • An bayyana kadan daga adadin kudaden da aka ware don yiwa majalisar kasar nan hidima a shekarar nan
  • A karon farko, shugaba Tinubu ya yi nasarar tsallake kasafin kudin 2024 a shekarar farko na mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - An ware Naira biliyan 3 don siyan litattafai na dakin karatun majalisar dokokin Najeriya a kasafin kudin 2024.

Wannan yana kunshe ne a cikin lissafin kasafi na 2024 da majalisar ta amince dasji a jiya Asabar 30 ga watan Disamba, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda bayanin kasafin kudin ya nuna, an kuma ware Naira biliyan 12.12 don hidimar dakin karatu na majalisar dokoki ta kasa.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa mu ka kara Naira Tiriliyan 1.2 a kasafin da Tinubu ya gabatar Inji Majalisa

Gwamnati ta ware biliyoyi don siyawa sanatoci da 'yan majalisa littatafai
Majalisa za ta siya littatafan biliyan 3 | HotoL GettyImages
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 3 domin aikin wurin ajiye motoci na majalisar dattawa da kuma wasu Naira biliyan 3 ga na majalisar wakilai.

An amince da kudurin kudin 2024

A ranar Asabar ne dai majalisun dokokin kasar biyu suka amince da kudurin kasafin kudin na shekarar 2024, inda suka kara yawansa daga Naira tiriliyan 27.5 da shugaba Bola Tinubu ya gabatar zuwa Naira tiriliyan 28.7.

A halin da ake ciki, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai, Abubakar Bichi, ya ce an kara kasafin da naira tiriliyan 1.27 saboda wasu dalilai, Daily Trust ta ruwaito.

A jawabinsa, ya fadi kadan daga dalilan da suka ja majalisar ta kara wani kaso na kasafin kudin da ake ta sa ran zai kawo sauyi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Ana rashin kudi, ‘yan majalisa sun kara Naira Biliyan 147 a kasonsu

Wannan ne kasafin kudin farko na shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu tun bayan karbar mulkin da ya yi a hannun shugaba Buhari.

Yadda gwamnati ta ware kudade a kasafin kudin bana

A tun farko, a rahoton Premium Times gano fahimci ‘yan majalisar tarayya sun yi wa kan su karin makudan kudi kan abin da za su kashe.

A maimakon N27.5tr da Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai sun maida kasafin 2024 ya zama N28.7tr.

An samu karin N1.2tr ne a daidai lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ta ke rokon mutane su yi hakuri da zafin tsare-tsaren tattalinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.