Gwamnan PDP Ya Bada Hutun Kwana 3 Kan Babban Rashin da Aka Yi a Najeriya, Bayanai Sun Fito

Gwamnan PDP Ya Bada Hutun Kwana 3 Kan Babban Rashin da Aka Yi a Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnan jihar Oyo ya ayyana hutun kwana uku na zaman makokin rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo
  • Makinde, mataimakin shugaban gwamnonin Najeriya tare da gwamnan Kwara sun ziyarci gidan marigayin na Ibadan
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Ondo ta shiga makokin kwanaki uku bayan rantsar da sabon gwamna, Lucky Aiyedatiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ayyana hutun kwanaki uku na zaman makokin mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu (SAN) na jihar Ondo.

Gwamna Makinde ya ayyana zaman makokin kwana uku a jiharsa ta Oyo domin jimamin wannan babban rashi da aka yi a Najeriya, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamna Makinde Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwanaki Uku a Jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Wannan umarnin na gwamna na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaimon Olarenwaju, ya rabawa manema labarai a Ibadan ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Karin hadiman gwamna 2 sun yi murabus daga muƙamansu, sun bayyana babban dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya bada wannan hutu ne awanni kaɗan bayan shi, tare da shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman sun ziyarci gidan marigayin na Ibadan.

Gwamnatin Ondo ta shiga makoki

Idan baku manta ba, gwamnatin jihar Ondo karkashin sabon gwamna, Lucky Aiyedatiwa, ta ayyana shiga zaman makokin kwanaki uku.

Ta ɗauki wannan mataki ne domin girmama marigayi Gwamna Akeredolu, wanda Allah ya yi ma rasuwa da safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023.

Babban sakataren yada labaran gwamna Aiyedatiwa, Ebenezer Adeniyan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba.

Makinde, mataimakin shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, ya zama na biyu da ya bada hutun kwanaki uku kan rasuwar Akeredolu, Vanguard ta ruwaito.

Yaushe za a binne marigayi gwamnan?

Iyalan mamacin sun tabbatar da rasuwar mai gidansu a wata sanarwa da ɗan Akeredolu ya fitar a madadin gidansu gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

A cewar sanarwan, nan gaba kaɗan gwamnatin jihar Ondo da kuma iyalai zasu fitar da cikakken bayanin yadda za a yi wa Akeredolu jana'iza da bikin binne shi.

Ƙarin Hadiman Gwamna 2 Sun Yi murabus a jihar Ondo

A wani rahoton na daban Hadiman tsohon gwamnan jihar Ondo wanda Allah ya yi wa rasuwa, Rotimi Akeredolu, sun ci gaba da yin murabus.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023, ƙarin wasu hadiman guda biyu suka yi murabus bisa dalilin mutuwar uban gidansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262