Karin Hadiman Gwamna 2 Sun Yi Murabus Daga Muƙamansu, Sun Bayyana Babban Dalili

Karin Hadiman Gwamna 2 Sun Yi Murabus Daga Muƙamansu, Sun Bayyana Babban Dalili

  • Hadiman tsohon gwamnan jihar Ondo wanda Allah ya yi wa rasuwa, Rotimi Akeredolu, sun ci gaba da yin murabus
  • A ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023, ƙarin wasu hadiman guda biyu suka yi murabus bisa dalilin mutuwar uban gidansu
  • Wannan na zuwa ne bayan kwamishinan ayyukan raya ƙasa, filaye da gidaje, Raimi Olayiwola Aminu, ya aje aikinsa nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Karin wasu hadimai biyu na tsohon gwamnan jihar Ondo, marigayi Rotimi Akeredolu, sun yi murabus daga kan muƙamansu.

Wannan sauyi da ake ta samu a gwamnatin jihar Ondo na zuwa ne awanni 24 kacal bayan mutuwar Akeredolu, wanda ya cika ranar Laraba a ƙasar Jamus.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu.
Karin hadiman marigayi Akeredolu 2 sun yi murabus daga muƙamansu a Ondo Hoto: Oluwarotimi Akeredolu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa hadiman da suka yi murabus yau Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023 sun haɗa da mai taimakawa na musamman kan ɗaukar hoto, Olawale Abolade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ragowar ɗayan shi ne babban mai taimakawa marigayi Akeredolu kan ayyuka na musamman da dabaru, Doyin Odebowale.

Hadiman Akeredolu sun fara yin murabus

Idan baku manta ba rahotonni sun bayyana cewa kwamishinan ayyukan raya ƙasa, filaye da gidaje na gwamnatin Akeredolu, Raimi Olayiwola Aminu, ya yi murabus.

Mista Aminu ya tabbatar da haka ne a wata wasiƙa da ya aike wa sakataren gwamnatin jihar Ondo.

A cewarsa matakin zai fara aiki daga yau Alhamis, 28 ga watan Disamba, 2023, kwana ɗaya kenan bayan mutuwar tsohon gwamna.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan babban alkalin jihar ya jagoranci rantsar da mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin sabon gwamnan jihar Ondo.

Kara karanta wannan

"Ba daɗi" Ɗan marigayi Akeredolu ya bayyana gaskiyar yadda gwamnan APC ya mutu, abun tausayi

Hakan ya biyo bayan mutuwar Akeredolu, wanda ya sha fama da jinyar ciwon kansa na tsawon lokaci a ƙasar Jamus, rahoton Daily Post.

Sai dai ana hasashen cewa wannan murabus da hadiman tsohon gwamnan suka yi ba zai rasa nasaba da tsamin alaƙarsu da sabon gwamnan ba a lokacin rikicin siyasar da aka yi a Ondo.

Shugaban APC ya koka kan rikicin Benue

A wani rahoton kuma Dakta Abdullahi Ganduje ya nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda rikici ya ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Benuwai.

Shugaban APC na ƙasa ya buƙaci bangaren Gwamna Alia, shugabannin jam'iyya da ƴan majalisar na jihar su hakura su haɗa kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262