Malamin Addini Ya Yi Hasashen Tsige Na Hannun Damar Tinubu, Gbajabiamila

Malamin Addini Ya Yi Hasashen Tsige Na Hannun Damar Tinubu, Gbajabiamila

  • Primate Babatunde Elijah Ayodele ya bukaci Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan shugaban kasa da ya yi addu'a kan makirai
  • Primate Ayodele ya ce wasu makirai na shirin tsige shi (Gbajabiamila) daga kan kujerarsa
  • A cewar malamin addinin, an rubuta sunan wani don maye gurbin babban dan siyasar wanda yake haifaffen jihar Lagas

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya zama mai sa ido sosai.

A wani sakon gargadi da ya saki a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, Primate Ayodele ya bayyana cewa ya gargadi na hannun damar shugaban kasar a baya.

Kara karanta wannan

Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje

Ya ce yana maimaita gargadin ne saboda jami'in gwamnatin da ake magana a kai yana iya fuskantar fushin Ubangiji nan take.

Primate Ayodele ya gargadi Gbajabiamila
Malamin Addini Ya Yi Hasashen Tsige Na Hannun Damar Tinubu, Gbajabiamila Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gbajabiamila na iya fuskantar wulakanci - Primate Ayodele

Jaridar Legit ta rahoto cewa har zuwa ranar 14 ga watan Yunin 2023, lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban ma’aikata, Gbajabiamila shine shugaban majalisar wakilai, inda ya kwashe shekaru hudu kan kujerar.

Shugaban cocin na INRI ya ce:

“Gbajabiamila, wannan sabon gargadi ne gare ka. Bam tsaneka ba, kuma ban tsani kowa ba.
"Ina dai fada maka ne kai tsaye, kamar yadda Ubangiji ya umarta. Don Allah ka nemi taimakon Allah. Suna so su wulakanta ka daga wannan kujera. Suna so su matsa maka lamba.
“Suna son haifar da gaba tsakaninka da Shugaban kasa – a kowane lokaci hakan na iya faruwa!

Kara karanta wannan

Tinubu ya lalubo tsohon Hadimin Atiku da ya ‘fasa kwai', ya ba shi mukamin Gwamnati

“Don Allah ka nemi taimakon Ubangiji kada hakan ya faru. Akwai sunan da zai karba daga hannunka. Ka sa ido, kuma a duba shi da kyau. Abu ne mai matukar girma.”

Ga wallafarsa a kasa:

Tinubu ya magantu kan Gbajabiamila

A wani labarin, mun ji a baya cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matsayarsa kan cece-kuce da ake kan shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila.

Tinubu ya bayyana haka ne a yau Litinin 30 ga watan Oktoba inda ya ce ya amince da gaskiyar Femi dari bisa dari kuma ya na da kwarin gwiwa a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng