Aiyedatiwa: An rantsar da Sabon Gwamnan Ondo Bayan Mutuwar Gwamna Akeredolu, Bayanai Sun Fito

Aiyedatiwa: An rantsar da Sabon Gwamnan Ondo Bayan Mutuwar Gwamna Akeredolu, Bayanai Sun Fito

  • Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya zama sabon gwamnan jihar Ondo bayan mutuwar Akeredolu
  • Sabon gwamnan ya karɓi rantsuwar kama aiki da yammacin yau Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023 a gidan gwamnati da ke Akure
  • Hakan na zuwa ne awanni bayan Gwamnatin Ondo ta tabbatar da rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu bayan fama da cutar daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamnan jihar Ondo ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan jihar.

Jaridar The Cable ta ce an rantsar da Aiyedatiwa a gidan gwamnati da ke Alagbaka, Akure, babban birnin jihar, bayan rasuwar gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.

Lucky Aiyedatiwa ya zama sabon gwamnan jihar Ondo.
Gwamnatin Ondo Ta Rantsar da Sabon Gwamna Lucky Aiyedatiwa Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Marigayi Gwamna Akeredolu ya rasu ne a kasar Jamus bayan fama da cutar daji yana da shekaru 67 a duniya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar Ondo ta tabbatar da haka a wata sanarwa da kwamishinar yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Misis Bamidele Ademola-Olateju, ta fitar.

Waɗanda suka halarci rantsar da sabon gwamna

Manyan jiga-jigan da suka halarci bikin rantsarwan sun haɗa da kakakin majalisar dokoki, Olamide Oladiji, sakataren gwamnatin jiha, Oladunni Odu da wasu mambobin majalisar zartarwa.

Shugaban ma'aikatan Ondo, Fasto Kayode Ogundele, tsoffin mataimakan gwamna, manyan sakatarori, da shugaban jam'iyyar APC na jihar, Ade Adetimehin, duk sun halarci bikin.

Daily Trust ta tattaro sauran waɗanda suka shaida rantsar da Aiyedatiwa wanda ya ƙunshi shugaban ma'aikatan marigayi tsohon gwamna, Chief Olugbenga Ale, magoya bayan APC da sauran su.

Da misalin karfe 5:15 na yamma Aiyedatiwa ya yi rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulki yayin da kuma yi rantsuwar shiga ofis da karfe 5:17 na yamma.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana ainihin silar mutuwar gwamnan APC, ta fadi babban halin gwamnan na kirki

Bugu da ƙari, Gwamna Aiyedatiwa, ya rattaɓa hannu kan takardar rantsuwar kama aiki da kusan misalin ƙarfe 5:19 na yammacin yau Laraba.

Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Gwamna Akeredolu

A wani rahoton na daban Shugaba Tinubu ya kadu bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a yau Laraba 26 ga watan Disamba

Tinubu ya bayyana Akeredolu a matsayin jajirtacce wanda ya ba da gudunmawa wajen kwato mulki a shari'ar zaben jihohin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel