Jam'iyyar PDP Ta Naɗa Sabbin Shugabanni 6 Bayan Wasu Sun Yi Murabus Sun Koma APC
- Watanni shida bayan murabus din wasu shugabannin PDP a jihar Imo, jam'iyyar ta naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu
- Jam'iyyar PDP ta sanar da naɗin sabbin mambobin kwamitin gudanarwa guda 6 da zasu cike gurbin waɗanda suka sauya sheka zuwa APC
- Wannan na zuwa ne wata ɗaya da ƴan kwanaki bayan PDP ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Imo da aka yi a watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a ranar Laraba da ta gabata ta sanar da naɗa mambobi 6 na kwamitin gudanarwa na jam'iyyar reshen jihar Imo.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ta naɗa sabbin shugabanni shida a jihar Imo ne domin cike guraben waɗanda suka yi murabus daga kan muƙamansu.
Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, watanni shida da suka wuce, wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jihar Imo suka yi murabus daga kujurensu na SWC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon haka ne jam'iyyar ta naɗa mutane shida da zasu maye gurabensu domin ci gaba da ayyuka yadda ya kamata.
Jerin sunayen mutanen da PDP ta naɗa a Imo
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da, Honorabul Solomon Onwuegbuchulem, a matsayin sakataren PDP na jiha da Prince Macdonald Enwere, a matsayin mataimakin sakatare na shiyyar Owerri.
Sauran sun kunshi Barista Chisimdi Nwandu, a matsayin mataimakin mai bada shawara kan harkokin shari'a da kuma Honorabul Ezeru Damian, a matsayin mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar Orlu.
Ragowar sune Lolo Ijeoma Domike a matsayin shugabar mata ta jiha da kuma Honorabul Anozie Udenwa, wanda a yanzu ya zama shugabam matasan PDP na Imo.
Idan za ku iya tunawa a ranar 8 ga watan Yuni, 2023, wasu shugabannin PDP suka sanar da yin murabus daga mukaminsu, inda daga bisani suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamnan PDP ya yi magana kan hukuncin kotun koli
A wani rahoton kuma Gwamna Peter Mbah ya yi martani jim kaɗan bayan kotun koli ta yanke hukunci kan nasarar da ya samu a zaben jihar Enugu.
A yau Jumu'a, 22 ga watan Disamba, kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta tabbatar da nasarar Mbah a zaben 18 ga watan Maris, 2023.
Asali: Legit.ng