Bayan Hukuncin Kotun Koli, Gwamnan PDP Ya Maida Martani Mai Jan Hankali Ga Talakawa

Bayan Hukuncin Kotun Koli, Gwamnan PDP Ya Maida Martani Mai Jan Hankali Ga Talakawa

  • Gwamna Peter Mbah ya yi martani jim kaɗan bayan kotun koli ta yanke hukunci kan nasarar da ya samu a zaben jihar Enugu
  • A yau Jumu'a, 22 ga watan Disamba, kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta tabbatar da nasarar Mbah a zaben 18 ga watan Maris
  • Mbah na jam'iyyar PDP ya yaba da hukuncin yana mai cewa lokaci ya yi da zai maida hankali kan ayyukan talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, a ranar Juma’a, ya yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar da ya samu a zaben 2023.

Gwamnan ya ce a yanzu abubuwan da ke ɗauke masa hankali sun kau, lokaci ya yi da zai nunka kokarin da yake na sauke nauyin al'umma da kuma bunƙasa jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Nazarin shekara: Shugaba Tinubu da wasu manya jigan-jigan siyasa da suka samu gagarumar nasara a 2023

Gwamnan Enugu, Peter Mbah.
Hukuncin Kotun koli: Hankali ya kwanta, lokacin aiki ya yi, Gwamna Mbah Hoto: Peter Mbah
Asali: Twitter

Mbah ya yi wannan furucin ne yayin yake martani kan hukuncin kotun koli a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Tuwita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mbah ya yabawa alkalan kotun ƙoli

A sanarwan, Gwamna Mbah na PDP ya ce:

"Muna mai mika tsantsar godiya ga alkalan kotun koli waɗanda suka bi diddigi suka tabbatar da adalci, muna ƙara miƙa godiya ta musamman gare su bisa kare haƙƙin mutane."
"Al'ummar jihar Enugu, wannan nasara da muka samu a shari'a taku ce, ina ƙara jinjinawa jajircewar ku. Goyon bayan da kuka bamu tare da addu'o'inku su ne tushen nasarar mu."
"Ba mu dauke su da wasa ba, amma a yanzu tunda waɗannan abubuwan ɗauke hankalin sun ƙare, lokaci ya yi da za mu ninka ƙoƙarinmu na yi muku hidima."

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar gwamnan PDP a zaben 2023

Abinda zamu sa a gaba - Mbah

Gwamna Mbah ya jaddada cewa a halin yanzu gwamnatinsa za ta maida hankali wajen samar da walwala, ci gaba da rayuwa mai sauƙi ga al'ummar jihar Enugu.

Mista Mbah ya kara da cewa:

"Zaku ga ladan goyon bayan da kuka bamu a ayyukan da suka shafi rayuwar talakawan jihar Enugu. Za mu kara mai da hankali kan jin dadin ku, ci gaba da rayuwa mai kyau."

Bincike Ya Tona Wanda Ya Bada Umarnin Canza Naira a Najeriya

A wani rahoton na daban Ana zargin tsohon gwamnan babban banki (CBN), Godwin Emefiele, da canza takardun Naira ba tare za amincewar Muhammadu Buhari ba.

Jim Obazee, mai binciken CBN mai zaman kansa wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ne ya bayyana haka a rahotonsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262