Karin Bayani: Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Gidan Gwamnatin Jihar PDP Kan Muhimman Abu 8
- Shiga tsakanin da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a rikicin jihar Ribas ya bar baya da ƙura
- Ɗaruruwan masu zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal ranar Jumu'a domin nuna adawa da yarjejeniya 8
- Zanga-zangar na zuwa ne bayan bidiyon kwamishinan ayyuka ya yaɗu inda aka ji yana cewa Tinubu ya tilasta wa Fubara sa hannu kan yarjejeniyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Jumu'a, 22 ga watan Disamba, 2023.
Zanga-zangar ta ɓalle ne kan sulhun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar, wanda a karshe aka cimma yarjejeniya 8.
A cewar rahoton Daily Trust, zanga-zangar ta nuna goyon baya ce ga Gwamna Siminalayi Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin waɗanda suka shiga wannan zanga-zanga
Bayanai sun nuna cewa masu zanga-zangar sun kunshi ɗalibai, ƙungiyoyin fararen hula, kungiyoyin kwadago da kuma wasu Hausawa mazauna jihar Ribas.
Tun da duku-duku, misalin karfe 7:00 na safiyar yau Jumu'a, tulin masu zanga-zangar suka mamaye gidan gwamnati da ke titin Azikwe a Fatakwal.
An ga masu zanga-zangar suna taruwa a wasu rumfuna da aka kafa a ƙofar shiga gidan gwamnatin, inda suka nuna adawa da yarjejeniya 8 da Fubara ya rattaɓa wa hannu.
Ko menene ya haddasa zanga-zangar?
Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, David Briggs, ya zargi Shugaba Tinubu da tilastawa Gwamna Fubara ya sa hannu a yarjejeniyar.
A wani bidiyo da Legit Hausa ta gani, Briggs ya yi ikirarin cewa yana ɗaya daga cikin masu ruwa da tsakin da suka halarci taron da aka yi a fadar shugaban ƙasa ranar Litinin.
Tsohon kwamishinan ya shaida wa manema labarai cewa Gwamna Fubara ya sa hannu kan yarjejeniyar ne bisa tursasawar da aka masa.
A cewarsa, duk masu zargin gwamnan ya kamata su binciki asalin mai ya faru a fadar shugaban ƙasa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya ce Shugaba Tinubu ya zo da rubutacciyar yarjejeniya, yana cewa wannan takarda ce matsayar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng