Nazarin Shekara: Shugaba Tinubu da Wasu Jiga-Jigan Siyasa da Suka Samu Babbar Nasara a 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - A tsarin jadawalin siyasar Najeriya, shekarar 2023 ce ta kama shekarar babban zaɓe, inda manyan jiga-jigan ƴan siyasa ke neman madafun iko.
Hakan na baiwa ƴan Najeriya batutuwa da dama da zasu yi mahawara a kai yayin da su kuma ƴan siyasa ke tsunduma yawon neman shawari da goyon baya.
Ƴan siyasar Najeriya musamman masu neman kujerun mulki su kan nemi shawari da goyon baya daga shugabannin siyasa, ƙungiyoyi da sarakuna domin cimma burinsu.
Bisa haka ne waɗanda dabarunsu suka hau daidai kuma da taimakon Allah, yanzu haka suna kan madafun iko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro muku manyan mutane uku da suka fi cin nasara a fagen siyasa a 2023, ga su kamar haka:
1. Bola Ahmed Tinubu
A saukaƙe zamu iya cewa yana ɗaya daga cikin ƴan siyasa masu kaifin basira da dabaru, Tinubu ya tsallake gargada da dama kana ya tsaya ya maida hankali kan burinsa na hawa kujera lamba ɗaya.
Sakamakon amfana da basirar Tinubu, banda wa'adi na biyu da APC ta samarwa Muhammadu Buhari a 2019, ta kuma lashe kujerun gwamnoni da mafi rinjaye a majalisar tarayya.
Bisa haka, mutumin da aka kira "zakin Bourdillon" da "jagaban Borgu" kuma ya taka rawa mai taken "Emi Lokan" jimlar yarbanci da ke nufin lokaci na ne a Abeokuta, masana sun ce babu mai iya dakatar da shi.
Wannan na ɗaya daga cikin abinda aka kalla a matsayin kwarjininsa a siyasa da kuma irin shirin da ya yi na tunkarar tseren zama mutum mai lamba ɗaya a ƙasar nan.
Bisa yadda ya gina siyasarsa a Kudu da Arewacin Najeriya, Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin APC a filin taron Eagle Square da ke Abuja ranar 8 ga watan Yuni, 2022.
Aiki tukuru da dabarun Tinubu sun haifar da ɗa mai ido yayin da ya lallasa manyan abokan takararsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP a zaben watan Fabrairu.
2. Nyesom Wike
Ko ƙaso shi ko ka tsane shi, haifaffen jihar Ribas, Nyesom Wike, na ɗaya daga cikin mutanen da za a iya bayyana su cikin kalmomi biyu: mai haddasa ruɗani da karfin hali.
Jigon jihar Ribas wanda aka yi wa laƙabi da dama, irin su ‘Zakin Ribas’, ‘Damisa mai ban tsoro’, da ‘Katafilar Ribas’ a yau ana daukarsa daya daga cikin manyan ‘yan siyasa a Najeriya.
Ministan Abuja na yanzu ya yi wa dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu aiki ne domin ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu saboda yana son mulki ya koma Kudu.
3. Abdullahi Umar Ganduje
Har zuwa yau, Abdullahi Ganduje ne ke samun nasara a faɗan siyasar da ke wakana tsakaninsa da tsohon ubangidansa, tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.
Tun bayan zaben 2019, rashin jituwa ta ƙara kamari tsakanin tsoffin abokan siyasan biyu, Kwankwaso da Ganduje, rikicin ya ci gaba da yaɗuwa har ya mamaye Kano.
Ganduje ya kwashe tsayon shekaru a matsayin mataimaki mai biyayya kuma na biyu a gidan siyasar Kwankwasiyya karkashin jagorancin Kwankwaso. Har ta kai ga ana masa kallon aminin Kwankwaso.
Kiɗan da rawar sun sauya ne yayin da Ganduje ya zaɓi zama mai zaman kansa bayan ya ɗare kan madafun iko a 2015. Daga nan faɗan ya soma har zuwa yau.
Yayin da Kwankwaso ya sha ƙasa a zaben shugaban ƙasa, Ganduje kuma ya zama shugaban jam'iyyar APC na ƙasa. Haka a shari'ar zaben Kano, APC ta yi nasara kan NNPP a kotuna.
Tinubu zai halarci gasar karatun Alqur'ani
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan baƙin da ake sa ran zasu halarci gasar karatun Alkur'ani Mai Girma na ƙasa a jihar Yobe.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Gwamna Zulum da takwaransa Mai Mala Buni na cikin waɗanda ake sa ran zasu halarci wurin.
Asali: Legit.ng