Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Nasarar Gwamnan PDP a Zaben 2023

Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Nasarar Gwamnan PDP a Zaben 2023

  • Yau Jumu'a 22 ga watan Disamba, 2023, kotun ƙoli ta tabbatar nasarar Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu
  • A hukuncin da suka yanke da murya ɗaya, kwamitin alkalai biyar na kotun koli sun kori ƙarar da ɗan takarar gwamna a inuwar LP, Chijioke Edeoga ya shigar
  • Legit Hausa ta tattaro cewa ɗan takarar ya shigar da ƙarar ne domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan Enugu da aka yi a watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Kotun ƙolin Najeriya, a ranar Jumu'a, 22 ga watan Disamba, ta tabbatar da nasarar Gwamnan jihar Enugu Peter Mbah na jam'iyyar PDP a zaben 2023.

Kamar yadda mai magana da yawun Mbah, Dan Nwomeh ya bayyana, kotun kolin ta warware dukkan batutuwan da suka shafi wanda ake kara na farko (Gwamna Mbah).

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotun ƙoli, Gwamnan PDP ya maida martani mai jan hankali ga talakawa

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah.
Yanzun Nan: Kotun koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar gwamnan PDP a zaben 2023 Hoto: Peter Mbah
Asali: Twitter

Wannan hukunci na nufin kotun wacce ake ma taken daga ke sai Allah ya isa ta kori ƙarar da ɗan takarar gwamna a inuwar Labour Party, Chijioke Edeoga, ya ɗaukaka zuwa gabanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tabbatar da hukuncin a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter, hadimin gwamnan ya ce:

"Kotun koli ta tabbatar da Gwamna Mbah a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Enugu."

Yadda shari'ar ta faro tun daga kotun zaɓe

A cewar kotun kolin, ba ta sami dalilin yin watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Enugu da kuma kotun daukaka kara da ke Legas ba.

Dukkan kotunan guda biyu sun yi fatali da korafe korafen da ɗan takatar LP ya ɗora kan nasarar Gwamna Mbah na jam'iyyar PDP.

Idan dai ba a manta ba a ranar 10 ga watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta Legas ta tabbatar da zaben gwamna Mbah.

Kara karanta wannan

Rusa zaben Abba Kabir: Jerin hukunce-hukuncen kotu 4 da suka bai wa kowa mutane a 2023

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta kori dukkan tuhume-tuhume uku da Edeoga ya gabatar a gabanta.

Manyan yan siyasan da suka yi nasara a 2023

A wani rahoton kuma Shugaba Tinubu ya ɗaya daga cikin ƴan siyasan da tauraruwar su ta haska a shekarar 2023 da ke bankwana

Mun zakulo muku akalla jiga-jigai uku da suka samu nasara mafi girma a rayuwarsu ta siyasa a wannan shekara da zata fita nan da kwanaki 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262