Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Wasu Yan Majalisar Tarayya da Gwamna APC a Arewa

Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Wasu Yan Majalisar Tarayya da Gwamna APC a Arewa

  • Rigima na neman ɓallewa tsakanin ƴan majalisun tarayya na APC da Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai
  • Tawagar ƴan majalisun APC da suka fito daga Benuwai sun caccaki Gwamna Alia da gudanar da mulkin kama karya mara tsari
  • Sun buƙaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gaggauta tsoma baki don kawo karshen lamarin kafin gwamnan ya gama da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Kwanaki kalilan bayan warware rikicin siyasar jihar Ribas, sabon rikici mai kama da shi ya barke a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya.

Ƴan majalisar tarayya daga jihar Benue na jam'iyyar APC sun caccaki Gwamna Hyacinth Alia da nuna halin mulkin kama karya da rashin iya jagoranci.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

Gwamna Alia na jihar Benuwai.
Yan Majalisar Tarayya Na Benue Sun Caccaki Gwamna Alia Na APC Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Sanata Titus Zam, shugaban ƴan majalisar tarayya na jihar Benuwai ne ya caccaki gwamnan yayin da yake jawabi a taron manema labarai ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Gwamna Alia ya haɗa kai da PDP'

Ya bayyana cewa Gwamna Alia ya hada kai da jam’iyyar adawa ta PDP domin ruguza jam’iyyar APC a jihar Benuwai, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sanatan ya soki Gwamna Alia da yin watsi da buƙatar APC kana ya naɗa duk wanda ransa ke so a muƙami da kokarin tsame yan majalisar tarayya daga harkokin jihar.

Haka nan kuma ya zargi gwamnan da tafiyar da mulki na mutum ɗaya a matsayin shi na gwamna kuma ba shi da wata manufa ta kawo ci gaba ga al'umma.

Sanata Zam ya bayyana abubuwa da dama da ƴan majalisar tarayya ke zargin Gwamna Alia da aikatawa na kawo koma baya da ruguza jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa na kulla yarjejeniya 8 da Wike", Gwamna Fubara Ya Magantu

Ya aike da sakon mafita ga shugaba Tinubu

Bayan haka kuma Sanatan ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kira Gwamna Alia domin ya shiga tsakani don warware abubuwan da ke faruwa.

A cewarsa, ya kamata Shugaba Tinubu ya gaggauta shawo kan lamarin tun kafin gwamnan ya kai ga rusa jam'iyyar APC a jihar.

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Ƙarancin Takardun Naira

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta baiwa ƴan Najeriya haƙuri kan karancin takardun kuɗin da ya dawo sabo a ƴan kwanakin nan.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammed Idris, ya ce matsalar da aka shiga ba da gangan aka kawo ta don kuntata wa mutane ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262