Kotun Kolin Najeriya Ta Tanadi Hukunci Kan Karar da Ta Nemi Tsige Gwamnan Jihar Bauchi

Kotun Kolin Najeriya Ta Tanadi Hukunci Kan Karar da Ta Nemi Tsige Gwamnan Jihar Bauchi

  • Kotun koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Bauchi wadda ɗan takarar APC ya shigar gabanta
  • Ta ce zata sanar da ranar da za a dawo ta yanke hukunci bayan kowane ɓangare ya gama jawabansa ranar Alhamis
  • Sadique Abubakar, ɗan takarar APC a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris ya nanata ma kotun cewa an tafka kura-kurai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta tanadi hukunta kan ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi a inuwar APC, Sadique Abubakar, ya kalubalanci nasarar Gwamna Bala Muhammed.

Gwamna Bala Muhammed da Sadique Abubakar.
Kotun koti ta tanadi hukunci kan karar da ta nemi tsige Gwamnan Jihar Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed @CAS_AMSadique
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa tun a baya kotun sauraron korafe-ƙorafen zabe da kotun ɗaukaka ƙara sun kori ƙarar ɗan takarar APC bisa dalilin rashin cancanta.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Tinubu a kotun koli ana shirin yanke hukunci kan zaben Kano

Air Vice Marshal Abubakar ya shaida wa kotu cewa mafi yawan takardun zaben da aka yi amfani da su a zaben watan Maris, ba a cike su yadda doka ta tanada ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana cewa ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na APC ya gaza gabatar da kwararan shaidu da zasu tabbatar da iƙirarinsa.

Yadda zaman kotun koli ya gudana

A zaman kotun koli na ranar Alhamis, lauyan Abubakar, J. Owonikoko, ya bukaci kotun da ta yi watsi da hukuncin karamar kotun.

Lauyan ya yi zargin cewa kotun ta gaza yin bayani kan takardun zaben da ba su da inganci waɗanda aka gabatar mata a matsayin shaida, The Nation ta ruwaito.

Lauyan hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, Mohammed N., ya shaida wa kotun kolin cewa kotunn zaɓe ta samu a wasu foma-fomai na zabe da ba a cike komai ba amma ba duka ba.

Kara karanta wannan

Kotun koli na shirin yanke hukunci, wasu tsageru sun yi yunƙurin ƙona gidan gwamnatin Kano

A nasa ɓangaren lauyan Gwamna Bala Muhammed, Chris Uche, ya bayyana ƙarar gaba ɗaya a matsayin wadda ba ta dace ba, yana mai cewa mai kara ya gaza gabatar shaida ko ɗaya.

Ya ce:

"Masu ƙara ba su gabatar da shaida ko ɗaya da zata yi bayani kan takardun zaben da suka gabatar ba, ina rokon kotu da ta kori wannan ƙara."

Bayan sauraron kowane bangare ne kwamitin alkalai biyar na kotun koli karkashin mai shari'a John Okoro, ya tanadi hukunci kan batun, ya ce za a sa ranar nan gaba.

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus

A wani rahoton na daban Honorabul Enema Paul ya yi murabus daga matsayin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Ƙogi.

A wasiƙar aje muƙamin da ya mika ranar Alhamis, Mista Paul ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali wajen kula da lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262