Kogi: Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki Ya Yi Murabus Kan Abu 1, An Naɗa Sabo Nan Take

Kogi: Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki Ya Yi Murabus Kan Abu 1, An Naɗa Sabo Nan Take

  • Honorabul Enema Paul ya yi murabus daga matsayin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Ƙogi
  • A wasiƙar aje muƙamin da ya mika ranar Alhamis, Mista Paul ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali wajen kula da lafiyarsa
  • Nan take majalisar ta zaɓi Nwuchiola a matsayin wanda zai maye gurbin kujerar mataimakin kakakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt. Hon. Enema Paul, ya yi murabus daga mukaminsa bisa dalilin rashin lafiya.

Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, mataimakin shugaban majalisar ya miƙa takardar murabus ɗinsa a zaman mambobi na ranar Alhamis.

Enema Paul ya aje kujerar mataimakin kakakin majalisa.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus Kan Rashin Lafiya Hoto: Enema Paul
Asali: Facebook

Ya yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa goyon bayan da ya ba shi, haka nan kuma ya nuna godiya ga majalisar dokokin bisa addu'o'i da taimakon da suka masa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi babban kamu, ɗan majalisar arewa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honorabul Paul ya bayyana cewa matsalar lafiyarsa ta fara ne a shekarar 2021, kuma da amincewar Gwamna Bello, ya tafi kasar waje domin neman magani da yi masa tiyata.

Duk da haka ciwon ba sauki kuma a kowace rana jikinsa na ƙara rauni. Duk da yana jinya a asibitin ƙasar waje, Mista Paul ya nuna buƙatar bada fifiko ga rashin lafiyar da ke damunsa.

Bisa haka ya nemi izinin Majalisar na tafiya kasar waje na tsawon shekara guda domin ci gaba da kula da lafiyarsa, sannan ya mika takardar murabus dinsa.

Majalisa ta zabi wanda zai maye gurbinsa

Bayan murabus din Paul, magatakardar majalisar, Mista Chogudo Sule Ahmed, ya yi kira da a gabatar da sunan sabon mataimakin kakakin majalisar.

Nan take Honorabul Abu Jibrin, mai wakiltar mazabar Ajaokuta, ya miƙe ya zaɓi Honorabul Ojoma Comfort Nwuchiola na mazabar Ibaji a matsayin sabon mataimakin.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

Honorabul Seyi Bello mai wakiltar mazaɓar Kabba/Bunu ya tashi ya mara ma wannan zaɓi baya, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Bayan haka magatakarda ya rantsar da Honorabul Nwuchiola a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kogi.

Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu

A wani rahoton na daban Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin alƙalai 11 da zasu cike wasu gurabe da ake da su a kotun kolin Najeriya

A zaman ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023, majalisar ta amince da naɗin bayan karɓan rahoto daga kwamitin shari'a

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262