Hotuna: Jami'ar APC Ta Yi Muhimmin Gyara a Kano Gabanin Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Abba

Hotuna: Jami'ar APC Ta Yi Muhimmin Gyara a Kano Gabanin Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Abba

  • Jam'iyyar APC ta sabunta ginin babbar sakateriyarta ta jihar Kano gabanin hukuncin kotun koli
  • Sakateriyar wadda ke kan titin Maiduguri a cikin birnin Kano, ta koma kamar sabuwa bayan gyaran da aka mata
  • Wasu hotuna da suka bayyana sun nuna yadda aka liƙa manyan hotunan shugaba Tinubu, Ganduje da Gawuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Kano ta canza sabon launi mai bam sha'awa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro ranar Laraba.

Sakatariyar wadda ke kan titin Maiduguri a cikin birnin Kano, babu ko hoton mutum ɗaya ɗaya a jikinta kafin yau amma a yanzu an ga zanen hotunan manyan ƙusoshi.

An sabunta sakateriyar APC ta Kano.
Sakatariyar APC a Kano ta canza kala yayin da ake dakon hukuncin kotun koli Hoto: Office of the APC National Chairman
Asali: Facebook

A yanzu an yi sakateriyar kwalliya da hotunan ɗan takarar gwamna, Nasiru Gawuna, shugaban jam'iyya na ƙasa, Abdullahi Ganduje da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa mutum 11 a kotun koli ana dab da yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano

Wannan sauyi a sakateriyar APC na zuwa ne awanni 24 gabanin fara sauraron shari'ar Abba Kabir Yusuf na NNPP da Gawuna na APC a kotun kolin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba, kotun sauraron kararrakin zabe da kotun ɗaukaka ƙara duk sun yanke hukuncin da ya baiwa jam'iyyar APC da Gawuna nasara.

Yadda aka yi kaca-kaca da sakateriyar APC

Bayan ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano ka ranar 19l8 ga watan Maris, 2023, wasu ƴan daba suka yi kaca-kaca da sakateriyar APC.

Duk wani abu da ke jikin ginin a wancan lokaci ko yake ajiye a ciki, ko dai yan daban sun sace ko kuma sun lalata shi.

Tun bayan faruwar haka, ginin sakateriyar ya koma karƙashin kulawar jami'an tsaro har zuwa lokacin da aka fara masa gyare-gyare.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

A halin yanzu, ginin ya koma kamar sabo da aka gina kwanan nan wanda ke ɗaukar hankalin duk wanda hanya ta biyo da shi ya zo wucewa.

Da yake tsokaci kan gyaran da aka yi, wani mamban APC a wurin ginin, ya ce an sabunta sakateriyar ne domin nuna sa ran nasarar Gawuna a kotun koli.

Hotunan yadda sakateriyar APC ta zama

Sakatariyar APC a Kano.
Sakatariyar APC a Kano ta canza kala yayin da ake dakon hukuncin kotun koli Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sakateriyar APC ta Kano.
Sakatariyar APC a Kano ta canza kala yayin da ake dakon hukuncin kotun koli Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Saƙatariyar APC a Kano.
Sakatariyar APC a Kano ta canza kala yayin da ake dakon hukuncin kotun koli Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Akpabio Ya Ayyana Kujerun Sanatoci 2 a Matsayin Babu Kowa

A wani rahoton na daban Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ayyana kujerun Sanatoci biyu a matsayin waɗanda babu kowa.

Kujerun da Akpabio ya bayyana a matsayin babu kowa sun haɗa da kujerar Sanatan Ebonyi ta kudu, Dave Umahi da Sanatan Yobe ta gabas, Ibrahim Gaidam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262