Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ayyana Kujerun Sanatoci 2 a Matsayin Babu Kowa
- Sanata Godswill Akpabio ya bayyana kujerun sanatan Ebonyi ta kudu da takwaransa na Yobe ta gabas a matsayin babu kowa
- Shugaban majalisar dattawan ya kuma buƙaci INEC ta shirya zaɓen cike gurbi domin maye gurbin kujerun guda biyu
- Dave Umahi da Ibrahim Geidam sun yi murabus daga kujerun ne bayan Shugaba Tinubu ya naɗa su a matsayin ministoci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ayyana kujerun Sanatoci biyu a matsayin waɗanda babu kowa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Kujerun da Akpabio ya bayyana a matsayin babu kowa sun haɗa da kujerar Sanatan Ebonyi ta kudu, Dave Umahi da Sanatan Yobe ta gabas, Ibrahim Gaidam.
Sakamakon haka ne majalisar dattawan ta buƙaci hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta shirya zaɓen cike gurbi domin maye gurbin kujerun guda biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Sanatocin 2 suka bar majalisar?
Dukkan sanatocin biyu, Umahi da Geidam, sun karɓi rantsuwar kama aiki yayin rantsar da majalisar dattawa ta 10 a watan Yuni amma daga bisani suka yi.murabus.
Sun yi murabus daga majalisar dattawa a watan Augusta bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa su a matsayin mambobin majalisar zartarwa.
A yanzu, Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi na riƙe da muƙamin ministan ayyuka yayin da Geidam ya karɓi kujerar ministan kula da harkokin ƴan sanda, cewar The Nation.
Minista ya yi murabus ya koma majalisa
A kwanan nan kuma tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya yi murabus daga kujerar ministan kwadago da samar da ayyukan yi na ƙasa.
Lalong ya ɗauki wannan matakin ne domim ya koma majalisar dattawa bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar masa da nasara a zaben Sanatan Filato ta kudu.
Tinubu ya naɗa alƙalai 11 a kotun koli
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya aike da wasika zuwa majalisar dattawa, inda ya nemi ta amince da naɗin sabbin alkalai 11 na kotun koli.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya karanta sakon Tinubu wanda ke kunshe da sunayen alƙalai 11.
Asali: Legit.ng