Daga Karshe, Yan Majalisar Dokoki Sun Ɗauki Sabon Mataki Kan Yunkurin Tsige Gwamnan PDP
- A karshe dai majalisar dokokin jihar Ribas ta janye shirinta na tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP
- Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan samun maslaha a zaman da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya jagoranta a Villa
- A zamansu na farko ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, ƴan majalisar sun janye sanarwan da suka aika wa gwamnan a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - ‘Yan majalisar dokokin jihar Ribas sun janye sanarwar yunkurin tsige gwamnan da suka aike wa Gwamna Siminalayi Fubara a kwanakin baya.
Mambobin majalisar dokokin sun koma bakin aiki, inda suka ci gaba da zaman majalisa a hukumance ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023 a Fataƙwal.
‘Yan majalisar dai sun taru ne kawai domin tattaunawa kan batun janye kudirinsu na tsige Fubara daga kujerar gwamnan Ribas, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya zauna da dukkan ɓangarorin guda biyu a fadarsa Aso Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Yayin wannan zama ne aka ƙulla yarjejeniya har guda takwas domin kawo ƙarshen rikicin siyasa kuma daga ciki harda dakatar da shirin tsige gwamna Fubara.
Majalisar dokoki da cika alƙawarin janye kudirinta
TVC ta rahoto cewa, ‘yan majalisar sun bayyana matakin janye kudirin tsige gwamnan ne a wata sanarwa da aka karanta a zauren majalisar ranar Laraba.
Sun bayyana cewa sun yanke wannan matakin ne domin girmama mai girma shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Rikicin da ya barke tsakanin Fubara da Nyesom Wike, wanda ya gada kuma ministan birnin tarayya na yanzu, ya raba mambobin majalisar gida biyu.
Wannan rikici ne ya sa mambobi 27 daga cikinsu suka sauya sheka daga Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
A cikin jerin abubuwan da suka faru a lokacin rigimar, ƴan majalisar da suka rabu gida biyu sun yi zama a wurare daban-daban, kwatsam sai kuma aka ji labarin shirin tsige gwamna.
Bayan haka kuma kwamishinoni da dama da ke goyon bayan Wike sun yi murabus daga gwamnatin Fubara.
Kakakin majalisar Ogun ya samu nasara a kotu
A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta raba gardama kan kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo.
Da take yanke hukunci, kotun ta tabbatar da nasarar kakakin majalisar kuma ta ci tarar ɗan takarar PDP wanda ya shigar da ƙara.
Asali: Legit.ng