Ministan Tinubu da Wasu Jiga-Jigai Na Cikin Babbar Matsala, Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Ɗau Zafi
- Shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa Wike zai gane bai fi karfin jam'iyya ba a lokacin da ya dace
- A cewarsa, ba tsohon gwamnan jihar Ribas ne kaɗai ya ci amanar PDP a babban zaben 2023 ba, akwai wasu kuma duk za a hukunta su
- Wannan magana na zuwa ne yayin da masu ruwa da tsaki ke ƙara kira ga PDP ta ɗauki matakin ladabtarwa kan Wike
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Muƙaddashin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, Umar Damagum, ya ce Nyesom Wike, ministan Abuja bai fi ƙarfin jam'iyya ba.
Damagum ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin tarayya Abuja ranar Talata, 19 ga watan Disamba, 2023, cewar jaridar Punch.
Ya bayyana cewa jam'iyyar PDP zata hukunta tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da sauran jiga-jigan da suka ci amanar jam'iyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu masu ruwa da tsakin PDP suka buƙaci Damagum ya ladabtar da Wike da wasu jiga-jigai bisa zargin zagon ƙasa ga PDP a zaɓen 2023.
Haka zalika, ana zargin Ministan babban birnin tarayya laifin haddasa rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Ribas, jihar da ke karkashin PDP.
"Zamu nuna wa Wike bai fi karfin PDP ba"
Channels tv ta tattaro cewa yayin da yake jawabi da yan jarida, Damagum ya ce:
"Matsayar mu kan batun Wike kamar yadda na sha faɗa ne. matuƙar kana nan a matsayin mamban PDP to ka sank komai yana da lokaci. Aikina shi ne gina jam'iyyar nan da na kawo hargitsi ba."
"Kuma bari na gaya muku wani abu, ba Wike kadai bane akwai wasu mutanen da suka yi mana zagon ƙasa. Idan muka kai wannan matakin za mu hukunta kowanen su."
"Idan Wike yana tunanin ya fi ƙarfin wannan jam'iyyar to mu kuma zamu nuna masa bai fi karfinta ba."
Shugaban PDP ya kara da cewa har yanzun Wike bai fito ya bayyana cewa ya bar babbar jam'iyyar adawa ba.
Jigon PDP ya buƙaci hukuncin ya shafi duk mai hannu
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani jigon PDP, Kabir Abdullahi, wanda ya nuna farin cikinsa da wannan kalamai na shugaban jam'iyya na ƙasa.
Sai dai a cewarsa, ya kamata uwar jam'iyya ta duba har a matakin jiha akwai waɗanda suka ci amanarta a zaben 2023, yana mai yin misali da Katsina.
Jigon ya ce:
"Mun daɗe muna jiran wannan lokaci, dama tuntuni ya kamata a hukunta mutane irinsu Wike a PDP, sai dai muna fatan abun ya gangaro har ƙasa domin akwai ire-irensu da yawa."
"A nan Katsina, zagon ƙasan da shugabannin PDP suka yi ne ya jawo mana, ya kamata abun ya zo har matakin gunduma, a hukunta duk mai laifi. muna goyon bayan 100 bisa 100."
Kwamitin gudanarwa na PDP ya yi taro a Abuja
A wani rahoton na daban Jagororin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan rikicin siyasar da ke wakana a jihar Ribas.
Rahotanni sun nuna cewa kwamitin NWC na PDP ta kasa ya nuna rashin yarda da yarjejeniya 8 da aka cimma na sasanta Wike da Fubara.
Asali: Legit.ng