Wike Vs Fubara: Shugabannin Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja Kan Abu 1

Wike Vs Fubara: Shugabannin Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja Kan Abu 1

  • Jagororin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan rikicin siyasar da ke wakana a jihar Ribas
  • Rahotanni sun nuna cewa kwamitin NWC na PDP ta kasa ya nuna rashin yarda da yarjejeniya 8 da aka cimma na sasanta Wike da Fubara
  • Wasu majiyoyi masu karfi sun ce ana sa ran a wannan taron na ranar Talata, PDP zata yanke matsayarta kan rikicin jihar Ribas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa (NWC) na Peoples Democratic Party (PDP) na taron gaggawa yanzu haka kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Ribas.

Shugabannin PDP na kasa sun shiga damuwa kan hanyar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bi wajen warware rikicin Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da wasu jiga-jigai na cikin matsala, Shugaban PDP na ƙasa ya ɗau zafi

Ministan Abuja da Gwamna Fubara.
Shugabannin PDP na Kasa Sun Shiga Ganawar Gaggawa Kan Rikicin Jihar Ribas Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Majiyoyi da dama sun shaida wa Daily Trust cewa ana sa ran wannan taron na yau Talata zai yanke matsayin jam’iyyar PDP kan rikicin da kuma hanyar da za a bi a warware.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Bola Tinubu ya sasanta Wike da Fubara

Idan baku manta ba a jiya Litinin, shugaban ƙasa Tinubu ya samu nasarar warware rikicin da ya haɗa bangarorin biyu, tsagin ministan Abuja Wike da ɓangaren Fubara.

A taron wanda masu ruwa da tsaki daga jihar Ribas suka halarta a fadar shugaban ƙasa, an cimma yarjejeniya takwas domin tabbatar da zaman lafiya.

Daga cikin yarjejeniyar da aka amince da su a zaman, an yanke cewa Martin Amaewhule ne zai ci gaba da jagorantar majalisar dokikin jihar Ribas kamar yadda aka kafa ta.

Haka nan kuma ƴan majalisa 27 da suka fice daga the Peoples Democratic Party (PDP) suka koma All Progressives Congress (APC), zasu ci gaba da zama a kujerunsu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan yarjejeniya 8 da Tinubu ya cimmawa tsakanin Wike da Fubara

Bugu da ƙari a yarjejeniyar an bai wa Gwamna Fubara da sauran muƙarrabansa umarnin su janye duk wata kara da suka shigar gaban kotu nan take, rahoton The Nation.

Gwamnan Jihar Benue Ya Sa Labule da Babban Hafsan Tsaro

A wani rahoton na daban Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai na ganawar sirri yanzu haka da babban hafsan tsaro na kasa a birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya isa hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) da misalin karfe 1:19 na tsakar rana yau Talata, 19 ga watan Disamba tare da muƙarrabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262