Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Tambuwal da Wamakko
- Sanata Aliyu Wamakko da Aminu Tambuwal sun san makomarsu a kotun ɗaukaka kara ranar Talata
- Kotun ta tabbatar da nasarar tsoffin gwamnonin jihar Sakkwato guda biyu a matsayin sanatan Sokoto ta kudu da arewa
- Haka nan kuma kwamitin alaƙalan kotun sun ci tarar waɗanda suka shigar da ƙara wasu adadin kuɗaɗe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Sokoto - Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar tsoffin gwamnonin jihar Sakkwato a zaɓen yan majalisar tarayya na 2023.
Kamar yadda Punch ta rahoto, kotun ta tabbatar da nasarar Aliyu Wamakko a matsayin sanata mai wakiltar Sokoto ta arewa a inuwar jam'iyyar APC.
Haka nan kuma a ɗaya ɓangaren, ta kuma tabbatar da nasarar Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Sokoto ta kudu a zaɓen 2023.
Tsohon sanatan Sokoto ta kudu, Ibrahim Danbaba, ne ya kalubalanci nasarar Tambuwal, ɗan takarar jam'iyyar PDP a gaban kotun yayin da tsohon mataimakin gwamna, Manir Dan’iya, ya kalubalanci Wamakko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci
Kwamitin alƙalai uku karkashin mai shari'a Mustapha Muhammad, yayin yanke hukunci, ya kori ƙarar Ɗanbaba kana ya ci tararsa N500,000 da za a baiwa Tambuwal da PDP.
Ɗaya daga cikin lauyoyin wanda ake ƙara da PDP, Suleiman Usman, ya ce kotu ta tabbatar da nasarar Tambuwal, kuma ta kori ƙarar da tsohon mataimakin gwamna ya kalubalanci Wamakko.
A rahoton Tribune, Usman ya ce:
"Kotu ta yanke hukunci kan zaben Sanatoci guda biyu na jihar Sokoto. Yayin da kotu ta tabbatar da zaben Sanata Tambuwal, alkalai uku sun kuma ci tarar wanda ya shigar da ƙara N500,000."
"Haka nan kotun ta kori ƙarar da aka shigar a madadin tsohon mataimakin gwamna, Manir Ɗan'iya mai kalubalantar Aliyu Wammakko, sanatan Sokoto ta arewa."
"Kotun ta ci tarar wanda muke karewa adadin wasu kudi da ba zan iya tunawa ba."
Kakakin Jam'iyyar APC Ya Samu Shirgegen Muƙami a Gwamnati
A wani rahoton kuma Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ogun ya samu babban muƙami a gwamnatin Dago Abiodun.
A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Disamba, Gwamna Abiodun ya naɗa Tunde Oladunjoye, a matsayin mai ba shi shawara.
Asali: Legit.ng