Kakakin Jam'iyyar APC Ya Samu Shirgegen Muƙami a Gwamnati, Gwamna Ya Jawo Shi a Jiki
- Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ogun ya samu babban muƙami a gwamnatin Dago Abiodun
- A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Disamba, Gwamna Abiodun ya naɗa Tunde Oladunjoye, a matsayin mai ba shi shawara
- Sabon mai ba gwamnan shawara kan harkokin midiya, Oladunjoye, ya riƙe mukamai da dama da suka shafi aikin jarida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya naɗa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas, Tunde Oladunjoye, a matsayin babban mashawarci kan harkokin midiya.
Wannan na kunshe ne a wata takardar naɗin muƙami nai ɗauke da kwanan watan ranar 11 ga watan Disamba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Takardar na ɗauke da sa hannun Gwamnan Abiodun kuma an aikata zuwa ga Mista Oladunye, wanda shi ne sakataren watsa labaran jam'iyyar APC na jihar Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina taya murna bisa wannan naɗi wanda ya dace da kai tare da fatan Allah ya taimake ka wajen tafiyar da harkokin ofis," in ji Gwamna Abiodun.
Taƙaitaccen tarihin sabon hadimin gwamnan
Kafin wannan naɗi, Oladunjoye ya riƙe mukamin mataimakin sakataren watsa labarai na sashjn sadarwa a kwamitin kamfen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.
Haka nan yana ɗaya daga cikin mambobin kwamitin yaɗa labarai a wurin zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC mai mulki.
Oladunjoye ya riƙe mukamai da dama da suka haɗa da, mamban majalisar gudanarwa ta kafar watsa labarai na jihar Ogun, da manba majalisar tafiyar da harkikin jami'ar Tai Solarin ta Ilimi (TASUED).
Bugu da ƙari, sabom hadimin gwamnan ya yi aiki a matsayin Shugaban Gidan Talabijin na Jihar Ogun (OGTV), kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Yan Najeriya sun fusata kan sasanta Wike da Fubara
A wani rahoton kun ji cewa Tsoma bakin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a rikicin siyasar jihar Ribas ya bar baya da ƙura a kafafen sada zumunta.
Wasu ƴan Najeriya sun nuna damuwarsu bisa yadda Gwamna Fubara ya aminta da yarjejeniyar da aka cimma a Villa da Wike.
Asali: Legit.ng