Kotu Ta Raba Gardama Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar Adamawa, Ta Ba da Kwararan Dalillai
- A karshe, Kotun Daukaka Kara ta raba gardama kan shari'ar zaben Gwamna Fintiri na jihar Adamawa
- Kotun da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP a matsayin zababben gwamna a jihar Adamawa
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani jigon jam'iyyar PDP kan wannan shari'a ta Kotun Daukaka Kara a Adamawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan zaben Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Kotun ta tabbatar da nasarar Fintiri na jami'yyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.
Wane hukunci kotun ta yanke a Adamawa?
Har ila yau, Kotun ta yi fatali da korafe-korafen Hajiya Aisha Binani ta jami'yyar APC saboda rashin gamsassun hujjoji, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun da ke zamanta a birnin Tarayya, Abuja ta yanke hukuncin ne a yau Litinin 18 ga watan Disamba.
Mai Shari'a, Tunde Oyebanji Awotoye ya yi watsi da korafe-korafen 'yar takarar ta APC da kuma jami'yyarta saboda rashin hujjoji kwarara.
Daga cikin hujjojin da kotun ta bayar shi ne rashin kawo shaidu kamar malaman zabe da su ke rumfunan zabe da aka gudanar, cewar Daily Post.
Wasu hujjoji kotun ta yi amfani da su?
Kotun ta ce jami'yyar APC da Binani kawai sun kira kwadinetocin kamfe ne wadanda ba sa wurin da ake gudanar da zaben a wancan lokaci.
Mai Shari'a, Awotoye ya ce wadanda jami'yyar ta kira a matsayin shaidu a kananan hukumomi 27 ba wadanda ke wakiltar jam'iyyar ba ne a rumfunan zabe.
Ya ce korafin da APC da Binani su ka shigar a gaban kotun bai cika ka'ida ba da har kotun za ta yi bincike a kai, inda kotun ta umarci jami'yyar APC da Binani su biya Ahmadu Fintiri naira miliyan daya.
Legit Hausa ta ji ta bakin jigon jam'iyyar PDP kan wannan lamari:
Aliyu Abubakar Abdulkadir wanda aka fi sani Kwamred Aliyu Dyer ya ce tun farko a bayyane ya ke Gwamna Fintiri ba tsaranta ba ne a siyasa tun da shi ya lashe zabe da mafi yawan kuri'u.
Ya ce:
"Tun farko ta so yin murdiya wurin ayyana ta wacce ta lashe zabe, da ba ta samu ba sai ta garzaya kotu saboda a tunaninta su ne da gwamnati a sama.
"Talakawan Adamawa sun yi ta addu'a don samun nasarar Fintiri saboda ya ci gaba da ayyukan alkairi da yake yi."
Aliyu wanda shi ne kwadinetan yanki na kungiyar NECAF ya ce wannan nasara bai rasa nasaba da irin jajirtattu da gwamnan ke da su kamar su Honarabul Adamu Atiku.
Ya kara da cewa akwai kuma sauran masu ba shi shawara ta gaskiya kuma iyaye kamar Alh Baba Kano Jada da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Kokarin jin ta bakin wani jigon APC a jihar, Habu Yola ya ci tura saboda bai mayar da martani kan sakon waya da aka tura masa ba.
Fintiri zai gwangwaje masu bautar kasa
A wani labarin, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa zai biya naira dubu 10 ko wace wata ga matasa masu bautar kasa a jihar.
Fintiri ya dauki wannan matakin ne don saukaka wa matasan halin kunci da ake ciki.
Asali: Legit.ng