Shugabancin Kasa Na 2027: An Zargi El-Rufai da Shirya Tuggu Don Kawo Cikas Ga Gwamnatin Tinubu

Shugabancin Kasa Na 2027: An Zargi El-Rufai da Shirya Tuggu Don Kawo Cikas Ga Gwamnatin Tinubu

  • Ana ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai yana shirya wani tuggu don kawo cikas ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Kungiyar Middle-Belt Patrotic Congress (MBPC) ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja
  • Sun yi zargin dansa, Bello Mohammed El-Rufai, wanda ke jagorancin kwamiti dokokin kula da bankuna, ana amfani da shi don karkatar da kudaden da aka tanadawa CBN don shirin neman shugabancin kasa da mahaifinsa ke yi

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT, Abuja - Kungiyar Middle-Belt Patrotic Congress (MBPC) ta yi zargin wani makirci da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke yi don amfani da kudade daga CBN don neman shugabancin kasa.

Kungiyar, yayin bayyana hakan a wurin taron manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba, ta ce a halin yanzu El-Rufai na neman goyon bayan manyan mutane daga arewa a kokarinsa na kawo cikas ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya bar mutane cikin duhu da ya ziyarci Janar Babangida bayan haduwa da Buhari, hotuna sun fito

An zargi El-Rufai da shiryawa Tinubu tuggu
Ana zargin El-Rufai na amfani da dansa Bello don shiryawa Tinubu makirci gabanin zaben shugaban kasa na 2027. Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba Jacob, shugaban kungiyar, ya yi nuni da cewa Bello Mohammed El-Rufai, shugaban kwamitin dokokin kula da bankuna, na cikin shirin yin amfani da CBN don samar da kudin yin aikin takarar shugabancin kasa na El-Rufai.

Sanarwar ta ce:

"Mun lura cewa el-Rufai, bisa halinsa, ya shirya yadda za a samu kudi domin wata kasuwanci nasa mai alamar tambaya, da ya ke boyewa karkashin kamfanin hannun jari, Afri-Venture Capital Company Limited, wacce za ta fara aiki a 2024, da $100 miliyan, fiye da N100 biliyan da zai yi amfani da shi don siye matasa, mafi yawanci matasan musulmi a matsayin wani mataki na ware kiristoci.
"Mun fahimci cewa matasan da ake tarawa da sunan koya musu sana'a, amma daga bisani za a yi amfani da su ne don zanga-zanga da za ta tsayar da kasa cak duk lokacin da el-Rufai ke bukata."

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

An yi bayanin alakar El-Rufai da CBN

Kungiyar ta yi ikirarin cewa matsayin dan El-Rufai wata hanya ce da za ta bai wa mahaifinsa damar juya dukiyar Najeriya ta hanyar babban bankin kasa.

Sun yi ikirarin cewa wannan damar da ya ke da shi za ta shafi tattalin arziki, suna gargadin abin da ka iya faruwa idan ya fito neman takarar shugabancin kasa a 2027.

Hakazalika, kungiyar ta yi kira ga shugabannin arewa, ciki har da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Janar Badamasi Babangida, su yi takatsantsan wurin harka da El-Rufai don tabbatar kasa ta zauna lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164