Tsige Gwamna Mutfwang Na Filato: APC Ta Fadi Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli
- Makomar tsigaggen Gwamna Caleb Mutfwang ya ta'allaka ne a hukuncin karshe da Kotun Koli za ta yanke kan takaddamar zaben jihar Filato
- Da yake magana a wata hira ta musamman da Legit, Williams Dakwom, jigon APC ya jaddada cewar Mutfwang, dan takarar PDP zai sha kaye a kotun
- Dakwom ya yarda cewa Kotun Koli za ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara, wacce ta tsige Mutfwang a matsayin gwamnan jihar Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Plateau, Jos - Wani mai nazari kan harkokin siyasa kuma jigon jam'iyyar APC, Williams Dakwom, ya jero manyan abubuwan da ka iya yin tasiri kan jam'iyyar PDP reshen jihar Filato a shari'ar da ke gudana a Kotun Koli.
Abba vs Gawuna: Kada ku cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan Kano - Shugabannin Hausawa a kudu
A wata hira ta musamman da jaridar Legit a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, ta wayar tarho, Dakwom ya jaddada cewa umurnin kotun na neman PDP ta gudanar da tarukanta, wanda suka saba, na iya tasiri a hukuncin karshe da Kotun Allah ya isa za ta yanke.
Jigon na APC ya yarda cewa Kotun Koli za ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara wajen tsige Mutfwang a matsayin gwamnan jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tsaka da takaddamar siyasar, jigon na APC ya bukaci PDP da Mutfwang da su ba da fifiko wajen bin umurnin kotun da ke kasa yayin da suke jiran hukuncin karshe na Kotun Koli.
Dakwom ya bayyana cewa:
"Batun shari'ar jihar Filato a Kotun Koli ba zai banbanta da hukuncin da kuka gani a kotun daukaka kara ba."
“Bari in bayyana muku a takaice na abin da yan kasarmu ba su da cikakkiyar masaniya a kai, saboda akwai umarnin da babbar kotun jihar Filato ta bayar cewa jam’iyyar PDP ta je ta gudanar da taronta, sun yi watsi da umarnin kotun kuma sun daukaka kara kan lamarin. Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da karamar kotun, kotun zabe ta yanke. Sun kuma shigar da karar zuwa Kotun Koli, amma sun kasa ci gaba da bibiyar karar da suka daukaka zuwa Kotun Koli, an yi watsi da karar don haka tun a wancan lokaci batunsu ya kasance kamar yadda yake a gaban kowace doka a kasar nan.
"Tunda ba su bi umarnin kotu ba, ba su da dan takarar kujerar gwamna a Filato.... Da farko ina ba su shawara da su je su bi umurnin kotu sannan su jira zabe na gaba."
Sarakuna sun nuna damuwa a shari'ar Kano
A wani labarin, mun ji cewa sarakunan Hausawa a Kudu maso Yamma sun gargadi shugabannin siyasa da kada su cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana fama da tashin hankali a Kano gabannin hukuncin da Kotun Koli za ta yanke a kan takaddamar zaben.
Asali: Legit.ng