Hankula Sun Tashi Yayin da Wike Ya Yi Wani Abu 1 Ana Tsaka da Rikicinsa da Gwamna Fubara

Hankula Sun Tashi Yayin da Wike Ya Yi Wani Abu 1 Ana Tsaka da Rikicinsa da Gwamna Fubara

  • Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara sun yi nesa da juna a wasu tarurruka na kwanan nan, wanda ke nuni da taɓarɓarewar dangantakarsu
  • Rikicin da ke tsakanin Wike da Fubara ya ta'azzara yayin da suka halarci taro daban-daban a Eleme da jami'ar jihar Rivers (RSU) inda suka zaɓi guje wa wata mu'amala
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin Wike wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne kuma ministan babban birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Rikicin jihar Rivers ya ɗauki wani salo na daban yayin da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya isa Port Harcourt domin gudanar da wasu ayyuka.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'ar arewa sun kuɓuta daga hannun yan bindiga, VC ya faɗi halin da suke ciki

Wike ya halarci jana'izar mahaifiyar Cif Ejor a Eleme, yayin da Fubara ke halartar taron yaye ɗalibai na jami'ar jihar Rivers (RSU).

Wike ya isa birnin Port Harcourt
Dangantaka na kara tsami tsakanin Wike da Gwamna Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Hankali ya tashi yayin da jiga-jigan siyasar biyu, da aka saba gani tare a taron jama'a, yanzu suke gujewa juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, a tawagar ministan akwai ƙaramin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, Sanata Barry Mpigi, Sanata Allwell Onyesoh, shugaban majalisar dokokin jihar Rivers, Manjo Jack da wasu ƴan majalisar masu biyayya gare shi.

Wike da Fubara sun nesanci juna

A wajen taron karo na 35 na jami’ar da ya gudana a ɗakin taro na Convocation Arena na jami'ar da ke Nkpolu-Orworukwo, Port Harcourt a ranar Asabar, Fubara, ya yi alƙawarin bunƙasa jami’ar tare da sanya ta ɗaya daga cikin mafi kyawu a cikin jami'o'in ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana zargin Shugaba Tinubu da rura wutar rikici a jihar PDP, bayani sun fito

Fubara ya yarda da tsarin da shugabannin jami'ar suka ɗauka don cimma nasara ciki har da samun cikakken izinin yin duk kwasa-kwasan da ake a jami'ar duk da ƙalubalen da aka fuskanta.

"Asalin ƙudurinmu na cigaban ilimi ya bayyana a kasafin kuɗinmu na 2024 inda ya samu kaso na uku mafi girma." A cewarsa.

Abin da aka saba gani a da, Wike da Fubara suna halartar tarurruka tare, yanzu ya koma suna nesantar juna da gangan, wanda hakan ya haifar da hasashe game da yanayin ƙawancen siyasarsu.

Fubara Ya So Yin Murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya so yin murabus daga muƙaminsa.

Kakakin ƙungiyar PANDEF ya bayyana cewa gwamnan ya so yin murabus saboda yadda Wike ya zame masa ƙarfen ƙafa wajen gudanar da mulkin jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng