Gwamna Fubara Ya So Yin Abu 1 Kafin Rikicinsa da Wike Ya Yi Kamari

Gwamna Fubara Ya So Yin Abu 1 Kafin Rikicinsa da Wike Ya Yi Kamari

  • Tsohon kakakin ƙungiyar Pan-Niger Delta Forum, Anabs Sara-Igbe, ya ce gwamnan Rivers, Sim Fubara ya so yin murabus daga muƙaminsa
  • Sara-Igbe ya ce Fubara ya yi tunanin zai sauka daga muƙaminsa ne saboda takun-saka tsakaninsa da ubangidansa, Nyesom Wike
  • A cewar shugaban na Neja Delta, Gwamna Fubara ba shi ba ne yake da iko kan kuɗaɗen jihar Rivers ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Kodinetan ƙungiyar shugabannin Kudu-maso-Kudu na ƙasa, Anabs Sara-Igbe, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ya yi tayin yin murabus daga muƙaminsa kafin rikicin jihar Rivers ya ƙara ƙamari.

Gwamna Fubara ya so yin murabus
Gwamna Fubara yin murabus daga mukaminsa na gwamna Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Da yake magana a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV, Sara-Igbe, tsohon kakakin ƙungiyar PANDEF, ya ce gwamnan ya yanke shawarar yin murabus ne saboda baya ga yadda na sama da shi suka hana shi walwala, ba shi da isasshen iko kan kuɗaɗen jihar kuma ya sha wahala wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana musabbabin abin da ya haddasa rikici tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Sara-Igbe ya yi zargin yin katsalandan a harkokin mulkin Rivers

Sara-Igbe ya bayyana cewa, amma da ba domin jam’iyyar PDP ta shiga tsakani ba, da Gwamna Fubara ya yi murabus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa:

"Kuɗaɗen da ke fitowa daga asusun tarayya, Wike ya haɗa kudin ne a kan wasu ayyuka, don haka idan kuɗin sun zo, sai banki su cire nasu su biya ƴan kwangila, tabbas ba mu san ko nawa ba ne kuɗin kwangilolin."
"Don haka sai gwamna ya ji 'ta yaya zan tafiyar da gwamnati alhalin ba ni da kayan aiki’, sai ministan ya fara jin haushin gwamnan, sai gwamnan ya ce, tunda haka ne bari na yi murabus. Dattawan PDP sun yi rinjaye a kan kada ya yi murabus, suna tunanin za a yi rikici.”

Onochie ta yi magana kan rikicin Rivers

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana zargin Shugaba Tinubu da rura wutar rikici a jihar PDP, bayani sun fito

A halin da ake ciki, tsohuwar shugabar hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC), Lauretta Onochie, ta ce Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin Wike da Fubara "saboda damuwa da jin dadin al'ummar jihar Rivers".

Onochie ta bayyana hakan ne ta wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a cikin ƴan kwanakin nan.

Dalilin Rikicin Wike da Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana abin da ya haddasa rikici a tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.

Wani na kusa da gwamnan ya bayyana cewa ƙarfa-ƙarfa aka riƙa yi wa gwamnan ta yadda aka mayar da shi ɗan kallo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng