Daga Karshe An Bayyana Musabbabin Abin da Ya Haddasa Rikici Tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Daga Karshe An Bayyana Musabbabin Abin da Ya Haddasa Rikici Tsakanin Wike da Gwamna Fubara

  • Rikicin siyasar jihar Rivers kullum ƙara ƙamari yake duk da ƙoƙarin sasanta ɓangarorin biyu da ake yi
  • Na kusa da Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana yadda Wike ya yi wa Gwamna Fubara ƙarfa-ƙarfa wajen naɗin muƙamai
  • A cewar na kusa da gwamnan dukkanin wasu masu muƙamai da aka naɗa Wike ne ya ba da sunayensu da muƙaman da za a ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - An bayyana musabbabin abin da ya haddasa rikici a tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da Nyesom Wike.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa Wike ne ya miƙa jerin sunayen kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da sauran manyan muƙamai da muƙamansu ga Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana zargin Shugaba Tinubu da rura wutar rikici a jihar PDP, bayani sun fito

An bayyana musabbabin rikicin Wike da Fubara
An bayyana yadda alaka ta yi tsami tsakanin Wike da Fubara Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wani makusancin gwamnan, wanda ya bayyana hakan, ya ce Fubara ba sa hannunsa a cikin naɗin, domin wanda ya gada shi ne ke da alhakin zaɓensu da naɗa su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kwamishinoni ke murabus a Rivers?

Majiyar ta ce murabus ɗin wasu daga cikin kwamishinonin ya tabbatar da cewa ba zabin gwamnan ba ne, amma Wike ne ya ɗora su, wanda ya ɗora Fubara a matsayin magajinsa.

A kalamansa:

"Eh, murabus ɗin kwamishinonin ya nuna ba gwamna ne ya naɗa su ba. Ba su kasance wadanda ya naɗa ba. Jerin sunayen kwamishinoni da mashawarta tsohon gwamnan ne ya miƙa wa gwamnan tare da ba da umarni kan mukamai da ofisoshin da za su zauna. Hatta jami’an tsaro an mika su ga gwamna tare da faɗin inda za a saka su.
"Shin ko akwai hanyar da gwamna zai iya naɗa kwamishinoni da masu ba da shawara da sauran su kuma su yi murabus irin haka? Ba zai yiwu ba. Kar ku manta cewa kusan watanni bakwai ne kawai a ofis. Kwamishinonin da gwamnan ya nada ba za su tafi ba.”

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gargadi masu rike da mukaman siyasa kan abu 1

Wike ya siya wa Gwamna Fubara fom

Da take mayar da martani ga iƙirarin da ministan ya yi na cewa gwamna da daukacin wadanda aka zaba a jihar Ribas ba su sayi fom din tsayawa takara da kuɗin aljihunsu ba, majiyar ya ce:

"Eh, tsohon gwamnan ya yi gaskiya da ya ce ya saya wa kowa fom ɗin. Amma ka yi addu'a, da wanne kuɗi? Kun san albashin gwamna kuma kun san kuɗin da ake kashewa wajen siyan fom ɗin takarar jam’iyyar PDP."
"Waɗanda ke son tafiya su tafi, gwamna zai tara ƴan tawagarsa, ba wai munafukai ba da aka dasa don leken asiri ga gwamnati ba."

An Zargi Wike da Wawushe $300m

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƴar majalisar tarayya daga jihar Rivers ta zargi Wike da wawushe $300m na aikin gyaran yankin Ogoni.

Boma Goodhead ta kuma yi iƙirarin cewa Wike ne ke da alhakin kisan da aka yi wa DPO na Ahoada ta Gabas, Bako Angbashim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng