Daga Ƙarshe, Gwamnan PDP Ya Bayyana Wanda Zai Marawa Baya a Zabe Mai Zuwa 2024

Daga Ƙarshe, Gwamnan PDP Ya Bayyana Wanda Zai Marawa Baya a Zabe Mai Zuwa 2024

  • Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana ɗan takarar da zai marawa baya a zaben gwamnan jihar mai zuwa a shekarar 2024
  • Obaseki ya ayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da mataimakinsa, Philip Shuaibu, wanda ke neman gaje shi
  • Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagun, ya ce dukkan masu ruwa da tsaki a jihar Edo sun amince zasu yi aiki tare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce zai goyi bayan duk wanda ya samu nasarar lashe tikitin takarar gwamnan na jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.

Gwamna Obaseki ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja a wurin taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP na kasa tare da masu ruwa tsakin Edo.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fara shirin tsige gwamna daga kan madafun iko kan abu 1 tal

Gwamna Obaseki ya ce yana tare da ɗan takarar PDP.
Zaben Edo: Zan mara baya ga duk wanda ya zama ɗan takarar PDP, Gwamna Obaseki Hoto: Godwin Obaseki, Philip Shuaibu
Asali: Facebook

Ya kuma ayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da mataimakin gwamna, Philip Shuaibu, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce:

"Ba bu wata matsala a tsakani na da mataimaki na, kuma yana nan wurin, ya shiga neman takara kuma ba wanda ya ji na umarce shi da ya janye. Shi ɗan asalin Edo ne don haka yana da damar shiga takara."

Shin wane ɗan takarar Obaseki zai mara wa baya?

Dangane da batun ɗan takarar da zai marawa baya a zaben gwamna mai zuwa a shekarar 2024, Gwamna Obaseki ya ce, "Zan goyi bayan duk wanda jam'iyyar PDP ta tsaida takara"

A nasa jawabin, mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa dukkanin masu ruwa da tsaki a jihar Edo sun amince za su yi aiki tare.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

A ruwayar Vanguard, Damagum ya ce:

“Mun amince mu yi aiki tare a matsayin tsintsiya daya, sabida haka za mu rarrabu zuwa kananan kwamitoci, ta yadda a karshe za mu fito da mafita mai kyau."

Shi ma da yake nasa jawabin, daya daga cikin ‘yan takarar, Asue Ighodalo, ya ce jam’iyyar PDP ta shirya tsaf domin lashe zabe mai zuwa a jihar ranar 21 ga watan Satumba, 2024.

Shugaban JAMB ya yi magana kan kwalin digiri

A wani rahoton kuma Shugaban JAMB ya buƙaci yan Najeriya su daina dogara cewa digiri zai sa su samu aiki a Najeriya a wannan zamanin.

Farfesa Ishaq Oloyede ya ce zamani ya canza, ba a buƙatar karatu a takarda, an fi kallon abinda zaka iya aikatawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262