Rikici Ya Ƙara Tsanani, 'Yar Majalisa Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Sauya Sheƙa Daga APC Zuwa PDP

Rikici Ya Ƙara Tsanani, 'Yar Majalisa Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Sauya Sheƙa Daga APC Zuwa PDP

  • Mamba mai wakiltar mazaɓar Okrika a majalisar dokokin jihar Ribas, Linda Somari Stewart, ta yi amai ta lashe kan sauya sheka zuwa APC
  • A ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2023 yan majalisa 27 da ke goyon bayan tsohon gwamna, Nyesom Wike, suka fice daga PDP zuwa APC
  • Sai dai rahotanni daga jihar Ribas sun nuna cews ƴar majalisar ya sake komawa PDP a hukumance kasa da wanni 48 bayan shiga APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Ɗaya daga cikin ƴan majalisa 27 na majalisar dokokin jihar Ribas da suka sauya sheka zuwa APC, Linda Somari Stewart, ta yi amai ta lashe.

Daya daga cikin yan majalisun Ribas ta lashe amanta.
Rikicin Rivers: Yan Majalisa Ta Yi Amai Ta Lashe, Ya Sakr Komawa PDP Daga APC Hoto: @emmaikumeh @excelength @GovWike
Asali: Twitter

A rahoton Sahara Reporters ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, Stewart, mai wakiltar mazaɓar Okrika, "ta canza shawara yayin da aka ayyana kujerun masu sauya sheƙar a matsayin ba kowa."

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake ofisoshi akalla 17 a sakateriyar ƙaramar hukuma 1 a jihar Kano

Wannan mataki da ta ɗauka ya nuna a fili cewa mambar majalisar tsallaka daga tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta koma bayan Gwamna Sim Fubara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma matakin ya tabbatar da cewa Stewart ta komaPeoples Democratic Party (PDP) kwanaki biyu kacal bayan ta shiga jam'iyyar APC, cewar rahoton Telegraph.

Yan majalisa 27 da ke goyon bayan Wike sun fice PDP

Tun da farko dai, ƴan majalisa 27 na majalisar dokokin jihar Ribas waɗanda suka yi ikirarin suna tare da tsohon Gwamna Wike, sun sanar za sauya sheƙa zuwa APC.

Mambobin majalisar sun fice daga PDP zuwa APC ne a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2023.

Sai dai wani lauya, Kalu Kalu, ya ce dukkan yan majalisa 27 da suka fice daga PDP a majalisar dokokin jihar Ribas kwanan nan sun rasa kujerunsu.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Rivers: Jigon APC ya yi wa Gwamna Fubara wankin babban bargo

A wata hira da Arise TV, lauyan ya bayyana cewa doka ta taɓadi cewa zababben shugaba da na ikon barin jam'iyyarsa zuwa wata ne kaɗai idan akwai rigimar shugabanci a jam'iyyarsa.

An rantsar da sabon ɗan majalisar APC a Legas

A wani rahoton na daban Majalisar dokokin jihar Legas ta rantsar da Age Suleiman a matsayin sabon mamba mai wakiltar mazaɓar Amuwo-Odofin.

Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya kori Olukayode Doherty na jam'iyyar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262