Ana Cikin Matsin Rayuwa, Gwamnan APC Ya Nada Sabbin Hadimai Sama da 150 a Jiharsa
- Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya naɗa sabbin masu taimaka masa na musamman guda 162
- A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Yinka Oyebode, ya fitar ya ce waɗanda aka naɗa zasu fara aiki ranar 1 ga watan Janairu
- Bayan haka kuma gwamnan ya kafa kwamitin mutum bakwai da zasu zaƙulo waɗanda za a naɗa a hukumomin gwamnatin Ekiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ekiti - Gwamna Biodun Oyebanji ya yi sabbin naɗe-naɗen hadiman da zasu kama masa wajen tafiyar da harkokin shugabanci a jihar Ekiti.
Vanguard ta ruwaito cewa Gwamna Oyebanji ya naɗa akalla manyan masu taimaka masa (SSA) guda 79, kananan masu taimaka masa (SA) 73 da masu ba shi shawara 10.
Hakan na kunshe a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Yinka Oyebode.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sabbin waɗanda aka naɗa zasu fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2023 kuma su ne rukuni na farko daga cikin rukunoni biyu na hadiman da za a naɗa.
Da yake taya su murna, Gwamna Oyebanji ya bukaci sabbin hadiman su ɗauki wannan a matsayin wata dama ta yi al'umma hidima da kuma taimakawa wajen kawo ci gaba.
Gwamnan ya kafa kwamitin mutum bakwai
Har ila yau, Gwamna Oyebanji ya amince da nada kwamiti mai ƙunshe da mutane bakwai domin kula da naɗe-naɗen da za a yi a hukumomin gwamnatin jihar Ekiti.
A rahoton Premium Times, sanarwan ta ce:
"Gwamna ya ɗora wa kwamitin nauyin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a faɗin kananan hukumomi 16, tantancewa da kuma bada shawarin mutanen da suka cancanta a naɗa a hukumomi."
"Ya kuma roƙi mambobin kwamitin da su yi biyayya ga doka yayin gudanar da aikinsu. Kwamitin na da wa'adin mako shida ya gama aikin kuma ya miƙa wa gwamna rahoto."
Dan takarar LP a jihar Edo ya sauya sheka
A wani rahoton na daban Dakta Dennis Aikoriogie, ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Edo a inuwar Labour Party ya fice daga jam'iyyar nan take.
Ɗan siyasan ya ce wasu daga waje da masu kuɗi sun mamaye jam'iyyar ta yadda har an jingine waɗanda suka wa LP bauta.
Asali: Legit.ng