Ana Shirin Zaben Gwamna a 2024, Dan Takara Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Adawa
- Dakta Dennis Aikoriogie, ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Edo a inuwar Labour Party ya fice daga jam'iyyar nan take
- Ɗan siyasan ya ce wasu daga waje da masu kuɗi sun mamaye jam'iyyar ta yadda har an jingine waɗanda suka wa LP bauta
- A wasiƙar murabus ɗin da ya aike wa shugaban LP, ya ce zai nemi takara a wata jam'iyyar ta daban
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Ɗaya daga cikin ƴan takarar da ke neman tikitin takarar gwamnan jihar Edo karkashin inuwar Labour Party, Dakta Dennis Aikoriogie, ya fice daga jam'iyyar.
Ya yi zargin cewa wasu shugabanni da ƙusoshin jam'iyyar LP sun nuna wanda suke so daga cikin yan takarar, bisa haka yake fargabar ba zasu yi adalci ba a zaɓen fidda gwani.
Haka nan Mista Aikoriogie ya yi zargin cewa wasu da suka shigo daga waje da masu buhunan kuɗi sun kwace jam'iyyar a halin da ake ciki, cewar rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, yanzu irinsa da suka bada kansu har suka gina LP ta kawo matsayin da take a yanzu a jihar Edo, su aka maida marasa amfani.
Aikoriogie ya aike da saƙon wasiƙar ficewa daga LP zuwa ga shugaban jam'iyya na gunduma ta tara a ƙaramar hukumar Egor a jihar Edo.
Ya kuma yi kwafin takardar ya tura ga shugaban Labour Party na ƙasa, da na jiha da na ƙaramar hukumar Egor, yana mai sanar da su cewa ya fice daga LP.
Wace jam'iyya zai koma?
A wasiƙar, ya bayyana cewa ya haƙura da takara a LP, zai nemi cika burinsa na siyasa a wata jam'iyyar ta daban, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wani ɓangaren wasiƙar ya ce:
"Ina mai sanar da cewa na yi murabus daga kasancewa mamban Laboour Party nan take. Hakan ta faru ne sakamakon gano inda jagororin jam'iyya suka dosa gabanin zaɓen gwamna a Edo."
"Bisa haka nake ganin ya dace na bar LP domin na nemi cika burina na siyasa a wata jam'iyyar daban, ina yi wa jam'iyya fatan alheri."
INEC ta rantsar da sabbin kwamishinoni 9
A wani rahoton kuma INEC ta rantsar da sabbin kwamishinonin zaɓe 9 daga cikin guda 10 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa.
Farfesa Mahmud Yakubu, wanda ya rantsar da su ranar Talata, ya ce za a rantar da ragowar ɗayan na jihar Akwa Ibom a 2024.
Asali: Legit.ng