Zaben Gwamnan Kogi: Dan Takarar APM Ya Kai Karar Ododo Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

Zaben Gwamnan Kogi: Dan Takarar APM Ya Kai Karar Ododo Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

  • Nasarar Usman Ododo a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi ta samu amincewar ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APM
  • Ododo, ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi da gagarumin rinjaye
  • Sai dai nasarar da ya samu ta fuskanci suka daga ɓangaren wasu ƴan takarar jam'iyyar adawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gamayyar ƙungiyoyin Middle Belt Groups ta bayyana cewa matakin da jam’iyyar APM da sauran jam’iyyun siyasa suka ɗauka ya tabbatar da nasarar Alhaji Usman Ododo, ɗan takarar jam’iyyar APC.

A cewar ƙungiyar, matakin da APM ta ɗauka na ƙin shigar da ƙara kan sakamakon zaɓen ya nuna cewa Ododo ya samu goyon bayan jama’a.

Kara karanta wannan

Kogi: SDP ta fadi dalili 1 da ya sa ta ki kalubalantar nasarar Ahmed Ododo

Dan takarar APM ya aminta da nasarar Ododo
Dan takarar APM ya amince da nasarar Ododo a zaben gwamnan Kogi Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

Dr Omale Ben Amedu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar kuma tsohon mataimakin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APM, ya yi watsi da rahotannin da ke ƙoƙarin ɓata sahihancin zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa APM ta amince da nasarar Ododo

Ya kuma jaddada cewa sakamakon da aka samu ya nuna ra'ayin jama'a.

A kalamansa:

"Sakamakon zaɓukan da aka yi a jihar Kogi nuni ne na ra'ayin jama’a, duk da cewa da yawa na iya ƙin amincewa da hakan, abu ne na al’ada, amma ya kamata mutane su koyi ɗaukar ƙaddara kan nasara ko shan kaye."
"Mun zaɓi kada mu je kotu ne saboda babu wani abu da za a yi muhawara a kai, an gudanar da zaɓukan a dukkan sassan jihar, ba a yi wani tsangwama ko cin zarafi ba."
"Jami’an tsaro sun hallara tare da tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, wanda ya haifar da wanda ya yi nasara kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka yi wa jami'an NDLEA kwanton bauna, bidiyo ya bayyana

Saƙo zuwa ga INEC

Dangane da haka, gamayyar ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta ƙara haɓaka kayan aikinta domin dacewa da yanayin gudanar da zaɓe da samar da sakamako.

"Mu na amfani da wannan kafar wajen yin kira ga masu ruwa da tsaki a jihar Kogi da su haɗa kai da wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar domin samun cigaba mai ɗorewa."

SDP Ta Hakura da Zuwa Kotu

A wani labarin kuma, jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta amince da nasarar da Ahmed Usman Ododo ya samu a zaɓen gwamnan jihar Kogi.

Jam'iyyar ta yi nuni da cewa ba za ta ƙalubalanci nasararsa a kotun zaɓe ba domin a bayyanae take shi ne zaɓin al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng