Kogi: SDP Ta Fadi Dalili 1 da Ya Sa Ta Ki Kalubalantar Nasarar Ahmed Ododo

Kogi: SDP Ta Fadi Dalili 1 da Ya Sa Ta Ki Kalubalantar Nasarar Ahmed Ododo

  • Sakamakon zaɓen gwamnan Kogi wanda Ahmed Usman Ododo ya lashe ya gamu da abubuwa da dama daga jam'iyyun adawa
  • Ɗaya daga cikin waɗannan al’amura shi ne tabbatar da cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen shi ne ra’ayin jama’a
  • Hakan ya fito ne a cewar wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar SDP, waɗanda suka zo na biyu a zaɓen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wakilan jam’iyyar SDP a jihar Kogi sun bayyana cewa jam’iyyar ta zaɓi ƙin shigar da ƙara kan nasarar zaɓaɓɓen Gwamna Ahmed Usman Ododo.

Sun jaddada cewa nasarar da Ododo ya samu a zaɓen ta yi daidai da zaɓin jama’a.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka yi wa jami'an NDLEA kwanton bauna, bidiyo ya bayyana

SDP ta amince da nasarar Ahmed Usman Ododo
Masu ruwa da tsaki na SDP sun gana da manema labarai a Abuja Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa, Honorabul Ayo Momodu, ya bayyana cewa shigar jam’iyyar SDP a zaɓen ya nuna irin gagarumin sha’awar da jama’a ke da shi a harkar zaɓe, tare da sanin waɗanda suka yi nasara da waɗanda suka faɗi zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Momodu ya bayyana yadda ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta SDP ta amince da sakamakon zaben cikin kwanciyar hankali, inda ya jaddada cewa nasarar da ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress ya samu a gaskiya yana nuna muradin al’ummar jihar Kogi.

SDP ta mika wuya ga nasarar Ododo

Momodu ya amince da gaskiyar abubuwan da ke faruwa kuma ya bayyana cewa duk masu ruwa da tsaki na SDP sun rungumi wannan gaskiyar.

A kalamansa:

"Jam’iyyar SDP ta sake duba matakin da ta ɗauka a baya ta hanyar amincewa da sakamakon zaɓen kamar yadda jama’a ke so, su ma al’ummar jihar Kogi sun nuna sha’awarsu na ɗaukar ƙaddararsu a hannunsu, wanda hakan ya bayyana a sakamakon zaɓen."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar Labour Party ta caccaki Peter Obi, bayanai sun fito

"Babu wani shakku kan cewa ɗan takaran da aka fi so ya lashe zaɓen, hakan kuma nuni ne da yadda jama'a ke son yin amfani da ƴancinsu na zaɓe na zaɓen shugabannin da za su yi aiki da muradun jihar wajen mayar da fatanmu da burinmu zuwa zahiri."

Momodu ya godewa shuwagabannin jam’iyyar Social Democratic Party bisa yadda suka ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya a duk lokacin babban zaɓe.

INEC Ta Magantu Kan Sakamakon Zaɓen Gwamnan Kogi

A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi amfani da “yawan tazarar da ke tsakani” domin tantance wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar 11, ga watan Nuwamba.

Hakan a cewar hukumar, ya sanya ta fasa gudanar da zaɓen cike gurbi na ranar 18 ga watan Nuwamba da ta shirya gudanarwa tunda farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng