Kwankwaso Ya Shirya Haɗewa da Shugaba Tinubu da APC, Ɗan Majalisar NNPP Ya Yi Bayani
- Abdulmumini Kofa ya musanta rahoton da ke cewa NNPP ta fara tattaunawar haɗa maja da PDP da wasu jam'iyyun adawa
- Ɗan majalisar tarayya ya jaddada cewa kofar NNPP a buɗe take ta yi aiki da kowa amma a yanzu babu wata tattaunawa da aka fara
- Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ya shirya addu'a ta musamman ga Tinubu da Kwankwaso a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya musanta jita-jitar cewa jam'iyyar NNPP na kokarin haɗa maja da PDP.
Maimakon haka ɗan majalisar tarayyan ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP a shirye take ta ƙulla ƙawance da jam'iyyar APC mai mulki ko wata jam'iyya daban.
Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta
Jibrin ya ƙara jaddada haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Manhajar X wadda aka fi sani da Twitter domin musanta rahoton cewa NNPP zata haɗa maja da PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulmumini Kofa ya wallafa a shafinsa cewa:
"An ja hankalinmu kan wasu rahotanni da ke yawo a kafafen watsa labarai cewa jam'iyyar mu mai albarka NNPP ta fara tattaunawa da PDP da wasu jam'iyyun domin haɗa maja."
"Ko ƙanshin gaskiya babu a wannan jita-jitar, ƙarya ce tsagwaronta. NNPP na nan a kan bakatarta cewa ƙofarta a buɗe take ta haɗa kai, ƙawance ko ma curewa guri ɗaya da APC, LP, PDP ko wasu jam'iyyu."
"Amma a halin yanzu babu wani kus-kus da aka fara kuma ko kaɗan jam'iyyar mu ba ta halarci wani taron kulla haɗaka ko maja da PDP ko wata jam'iyya ba.
"Wannan rahoton da ake yaɗawa aiki ne na wasu gurɓatatun mutane wanda ya kamata mutane su lura."
Kofa ya tabbatar da yana ɗasawa da Tinubu
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ɗan majalisar ya jagonranci taron addu'o'i na musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso.
A jawabinsa na wurin taron wanda aka sauke Alƙur'an sama da sau 1000, Kofa ya ce dangantakar da ke tsakaninsa da Shugaba Tinubu a fili take.
Kwamishina Ya Tabbatar da Ana Jabun Sa Hannun Gwamnan
A wani labarin na daban Alamu sun ƙara tabbatar da cewa wasu muƙarraban gwamnatin Ondo suna yin jabun sa hannun Gwamna Rotimi Akeredolu
Kwamishinan makamashi, Razaq Obe, ya tabbatar da haka a wata wasiƙa da ya aike wa mataimakin gwamna, Lucky Ayedatiwa
Asali: Legit.ng