Gwamnan APC Zai Yi Murabus Daga Madafun Iko Kan Rashin Lafiya? Gaskiya Ta Bayyana
- Har yanzu ana ta takaddama kan yanayin rashin lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo
- Yayin da wasu ke ganin ya kamata ya yi murabus saboda rashin lafiya, Gwamnatin Ondo ta ce gwamna na yin aikinsa
- Kwamishinar yaɗa labarai ta ce har yanzun gwamnan bai gaza aiki ba, kawai ya daina halartar taruka da bukukuwa ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Kwamishinar yada labarai da wayar da kan jama’a a jihar Ondo, Mis Bamidele Ademola-Olateju, ta bayyana dalilin da ya sa Gwamna Rotimi Akeredolu (SAN) ba zai yi murabus ba.
Wannan na zuwa ne yayin da masu ruwa da tsaki a jihar suka buƙaci gwamnan ya yi murabus ko ya miƙa karfin iko ga mataimakinsa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
Amma kwamishinar yaɗa labaran ta ce har yanzun Gwamna Akeredolu bai gaza ba duk da rashin lafiyar da yake fama da ita, don haka babu buƙatar ya yi murabus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ademola-Olateju ta yi wannan bayani ne a wata hira da ta yi da Arise tv da safiyar ranar Jumu'a, 8 ga watan Disamba, 2023
Har yanzu dai batun lafiyar gwamnan na ci gaba da jan hankali da haddasa kace-nace musamman saboda yadda ya koma zama a gidansa na kai da kai da ke Ibadan a jihar Oyo.
Gwamnan ya ci gaba da zama a Ibadan tun lokacin da ya dawo daga ƙasar Jamus a watan Satumba, bayan shafe sama da watanni uku yana jinya, cewar Daily Trust.
Meyasa gwamnan ba zai yi murabus ba?
Da take jawabi kan batun rashin lafiyar, kwamishinar yaɗa labaran ta ce har yanzu gwamnan yana ayyukan da suka rataya a wuyansa bai gaza ba.
A cewarta, abubuwan da za a iya cewa Gwamna Akeredolu ba ya gaza yi a yanzu ba su wuce halartar taruka da bukukuwa na yau da kullum kamar ɗaurin aure ba.
Da aka tambaye ta ko Akeredolu ya yi tunanin murabus kamar yadda lokacin yana shugaban ƙungiyar lauyoyi (NBA) ya nemi marigayi Umaru Yar’Adua ya yi murabus, kwamishinar ta ce:
"Gwamna bai gaza ba, har yanzu ina nan a kan bakata, yana yin abin da ya kamata cikin sauki, babu wata matsala, kawai siyasa ce ta sa ake kambama abun."
NNPP da APC sun rattaɓa hannu kan yarjejeniya a Kano
A wani rahoton na daban Manyan jam'iyyu biyu masu adawa da juna a jihar Kano, NNPP da APC sun sake sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Jam'iyyun biyu sun yi haka ne ranar Jumu'a domin tabbatar da zaman lafiya gabanin, lokacin da kuma bayan hukuncin kotun koli.
Asali: Legit.ng