Tsagin Abba da Gawuna Sun Rattaɓa Hannu Kan Muhimmiyar Takarda a Kano Gabanin Hukuncin Kotun Koli

Tsagin Abba da Gawuna Sun Rattaɓa Hannu Kan Muhimmiyar Takarda a Kano Gabanin Hukuncin Kotun Koli

  • Manyan jam'iyyu biyu masu adawa da juna a jihar Kano, NNPP da APC sun sake sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
  • Jam'iyyun biyu sun yi haka ne ranar Jumu'a domin tabbatar da zaman lafiya gabanin, lokacin da kuma bayan hukuncin kotun koli
  • A yanzu dai Gwamna Abba Kabir ya ɗaukaka kara zuwa kotun koli bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tsige shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Yayin da ake tunkarar hukuncin kotun koli kan zaben gwamnan jihar Kano, manyan jam'iyyu biyu sun ƙara jaddada matsayar tabbatar da zaman lafiya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa NNPP ta Abba Kabir Yusuf da APC ta Nasir Gawuna sun sake rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin, lokacin da bayan yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Abba Vs Gawuna: 'Yan sanda sun roki malaman addini su dage da yin wa'azi kan tada tarzoma a Kano

Gwamna Abba Kabir da Yusuf Gawuna.
Kotun koli: NNPP da APC Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr Nasiru Gawuna
Asali: Facebook

Jam'iyyun biyu, NNPP da APC sun rattaɓa hannun ne ranar Jumu'a gabannin fara taron kwamotin tsaro na jihar Kano a hedkwatar rundunar ƴan sanda reshen jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Juma’a, 8 ga watan Disamba, shugabannin tsaro da jagororin jam’iyyun siyasa suka sake zama domin nazari tare da sabunta alkawarin zaman lafiya.

Da yake hira da ‘yan jarida, kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Mohammed Usaini Gumel ya ce:

"Muna kara yaba wa shugabannin NNPP da APC bisa yadda suka tsaya tsayin daka kan yarjejeniyar zaman lafiya a karo na uku tun bayan da suka rattaba hannu kan kudirin."

NNPP da APC sun jaddada kudirin zama lafiya

A nasa jawabin, shugaban NNPP a jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce jam'iyyar su ba ta haɗa hanya da rikici ba kuma basu ƙaunar duk abinda zai ruguza zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wasu muhimman takardun ƙarar zaben gwamnan Arewa da ke gaban kotu

"A namu bangaren, za mu yi duk mai yiwuwa don ganin jiharmu ta ci gaba da zama lafiya da kwanciyar hankali," in ji shi.

A rahoton Daily News, yayin da yake nasa jawabin, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Shehu Maigari ya ce:

“APC jam’iyya ce mai ƙaunar zaman lafiya, haka take a koda yaushe. Ga masu cewa za su samu duk abin da suke so ta hanyar tashin hankali Allah yana kallo kuma shi ne shaida.
"Yarjejeniyar zaman lafiya da muka sanya hannu a baya, muna kan ta kuma za mu ci gaba da yi mata biyayya."

Gwamnatin Ogun ta sa ladan N50m kan makasan hadimin gwamna

A wani rahoton na daban Gwamnatin Ogun ta sanya ladan N50m ga duk wanda ya taimaka da bayanan sirri har aka kama makasan daraktan kuɗi.

Kusan mako biyu da suka wuce wasu yan bindiga suka kashe hadimin gwamnan a hanyar komawa ofis, suka sace makudan kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262