Ministan Shugaba Tinubu Ya Fice Daga Jam'iyyarsa, Ya Shirya Taron Shiga APC

Ministan Shugaba Tinubu Ya Fice Daga Jam'iyyarsa, Ya Shirya Taron Shiga APC

  • Ministan wutar lantarki a Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da aniyarsa ta komawa jam'iyyar APC
  • Adebayo Adelabu, wanda ya riƙe tutar takarar gwamnan Oyo a inuwar Accord Party a zaben 2023, ya tabbatar da haka a wata wasiƙa da ya aiko wa Legit Hausa
  • Ministan ya ce za a yi bikin sauya shekarsa ne ranar Jumu'a ta mako mai zuwa kuma hakan ya biyon bayan ganawarsa da jagororin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Ministan wutar lantarki na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Adebayo Adelabu, ya fice daga jam'iyyar Accord Party zuwa APC mai mulki.

Ministan wutar lantarki zai koma APC.
Ministan Shugaba Tinubu Ya Fice Daga Jam'iyyarsa, Zai Koma APC Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wani saƙo da jigon jam'iyyar APC a jihar Oyo, Akin Akinwale, ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa yayin da aka zargi Tinubu da haddasa rikicin siyasa a Kano

Jigon ya wallafa takardar gayyata zuwa bikin sauya shekar Ministan, wanda zai sake komawa jam'iyyar APC mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adelabu ya shirya gagarumin bikin komawa APC

A wasiƙar, Mista Adelabu ya bayyana cewa za a gudanar da gagarumim bikin dawowarsa jam'iyyar APC ranar Jumu'a, 15 ga watan Disamba, 2023.

Ya kuma bukaci dukkanin shugabannin jam'iyyar APC na kananan hukumomin jihar Oyo da mambobin majalisar zartarwa su halarci taron.

Ministan ya kuma tuna cewa tun usuli ya bar APC ne saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye reshen jihar Oyo da kuma rashin gamsuwa da zaben fidda ɗan takarar gwamna.

Meyasa zai koma APC a yanzu?

A cewarsa, ya yanke shawarin sake komawa gida APC ne bayan zaman neman shawari da shugabannin APC na ƙasa, bisa haka ya ga lokaci ya yi.

Adelabu ya ce:

"Mataki na farko da na fara ɗauka shi ne ziyarar ban girma da na kaiwa shugabam APC na ƙasa, inda muka amince cewa dole na dawo jam'iyya mai mulki."

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi dalili 1 da ya sa masu ruwa da tsakin jam'iyyar suka tabbatar da korar Kwankwaso

Wani jigon APC a jihar Katsina, Usman Ahmad, ya faɗa wa Legit Hausa cewa suna maraba da matakin ministan amma dama ya kamata duk ministan da ba ɗan APC ya dawo APC.

Usman, tsohon ɗan takarar kansila a APC ya ce:

"Wannan ya yi daidai, dama asali ɗan APC ne kuma ya fita ne saboda burinsa na takarar gwamna bai cika ba, yanzu ya samu Minista, kaga ya kamata ya dawo."
"Mu a APC muna maraba da kowa, kuma ina mai tabbatar maka a nan yakin mu muna namu kokarin na ganin mun ƙara ƙarfafa jam'iyyarmu mai farin jini," in ji shi.

Ganduje Ya Shiga Ganawar Sirri da Gwamna Mai Mala Buni

A wani rahoton na daban Jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta shiga wata ganawar sirri da wasu gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar a Abuja.

Kadan daga cikin mahalarta taron sun hada da gwamnan jihar Imo, Nasarawa, Yobe da mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262