APC Ta Nuna Yatsa Kan Wanda Take Zargi da Kai Mummunan Farmaki Gidan Kwamishinan Zabe a Kogi
- Kungiyar kamfen din APC ta yi zargin cewa yan daban jam'iyyar SDP ne suka kai farmaki gidan kwamishinan zaben na jihar Kogi
- Kingsley Femi Fanwo na APC wanda ya yi jawabi a taron manema labarai, ya yi ikirarin cewa yan barandar sun kuma yi yunkurin kona gidan gwamnatin jihar Kogi
- Saboda haka APC ta bukaci jami'an tsaro da su dauki mataki kan halin dan takarar gwamnan SDP a zaben da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba, Murtala Ajaka
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Lokoja, jihar Kogi - Jam'iyyar APC ta daura alhakin harin da yan bindiga suka kai gidan kwamishinan zabe na jihar, Gabriel Longpet kan jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Kingsley Fanwo, kakakin kungiyar kamfen din APC, wanda ya yi jawabi a wani taron manema labarai a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba, ya ce yan bindihar sun kuma yi yunkurin kona gidan gwamnatin jihar Kogi.
'SDP na tafiyar da gungun masu aikata laifuka' - APC
A cewar Fanwo, dan takarar gwamna na jam'iyyar SDP, Murtala Yakubu Ajaka, da magoya bayan SDP sun nuna kwakkwarar shaidar cewa su mutane ne masu rikici kuma ya kamata a rike su kan abun da ya faru a gidan kwamishinan zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Nation ta nakalto jam'iyyar ta APC tana cewa:
"Ba mu da matsala da ba tawagar lauyoyi damar duba takardu da kayayyaki. Al'ada ce. Amma ba za mu bari kowani dan siyasa mai shan jini ya yi wadaka da ainahin hukuncin da mutanen Kogi suka yanke ba.
"Muna ganin ta'asar da dan takarar SDP da aka kayar da gungun masu aikata laifinsa suka aikata. Sun shigo da yan daba cikin Kogi daga jihohi masu makwabtaka."
A halin da ake ciki, jaridar Blueprint ta rahoto cewa jam’iyyar APC ta bukaci yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta cafke Ajaka.
Yan bindiga sun farmaki gidan kwamishinan zabe
A baya mun ji cewa yan bindiga sun kai mummunan hari gidan kwamishinan zabe a Lokoja da ke jihar Kogi.
Legit ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na daren yau Juma’a 1 a watan Disamba.
Asali: Legit.ng