Abun Bakin Ciki Yayin da Fitattun Tsoffin Yan Majalisa 2 Suka Mutu Cikin Awanni 48
- Tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Alajagusi Abdulyekeen Sadiq, ya riga mu gidan gaskiya
- Takwaran Sadiq a jihar Kwara, tsohon dan majalisar wakilai Yinusa Yahya, shima ya rasu a farkon makon nan, lamarin da ya jefa al'umma cikin bakin ciki
- A wata sanarwa da Legit Hausa ta gano, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRasaq, ya yi alhinin mutuwar yan siyasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ilorin, jihar Kwara - Allah ya yi wa wasu tsoffin yan majalisar dokokin tarayya da suka wakilci jihar Kwara a majalisar wakilai, Yinusa Yahya da AbdulYekeen Sidiq Alajagusi, rasuwa.
Alajagusi wanda aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki yayin da yake gadon asibiti don ya wakilci mazabar Asa/Ilorin ta Yamma a 2019 bai warke ba daga halin rashin lafiya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
N27.5tr: Majalisar wakilan tarayya da Sanatoci sun fara tafka mahawar kan kudirin kasafin kuɗin 2024
Tsohon mamba na jam'iyyar PDP kafin ya koma APC, Alajagusi ma ya rasu a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi Yahya, wanda ya yi dan majalisa mai wakiltar mazabar Moro/Edu/Patigi, ya kasance shugaban kwamitin majalisa kan ayyuka, amma ya fadi takarar kujerar sanata inda ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar Kwara, Alhaji Shaba Lafiaji.
Lafiajiya lashe zaben fidda gwani na PDP da aka yi a yankin Bode Saadu a 2007.
Marigayin ya kasance tsohon shugaban kwamitin kwalejin fasaha ta jihar Kwara kuma daga baya ya koma jam’iyyar APC har zuwa rasuwarsa a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.
Gwamnan Kwara ya yi alhini
A sakon ta'aziyyarsa a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, Abdulrahman Abdulrazaq, gwamnan jihar Kwara, ya nuna bakin cikinsa kan mutuwar tsoffin yan majalisar tarayyar biyu.
Yayin da gwamnan ya bayyana Alajagusi a matsayin wanda ya daga murya a fafutukar Ó Tó Gẹ́, ya ce 'Bulldozer', kamar yadda ake kiran Yahaya ya kasance "babban masanin harkokin siyasa mai kyakkyawar niya ba wai ga Edu, karamar hukumarsarsa kadai ba amma ga fadin jihar gaba daya.
Gwamnan ya roki Allah ya sakawa yan siyasar biyu da aljannah. Ya kuma aika sakon ta'aziyya ga iyalansu.
Shugaban NUGA ya kwanta dama
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Mista Emeka Ogbu, Shugaban Kungiyan Shirya Wasannin Jami'o'i na Najeriya (NUGA), ya riga mu gidan gaskiya.
Farfesa Mohammed Bawa, mukadashin shugaban kungiyar, ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Laraba a Jos, babban birnin jihar Filato.
Asali: Legit.ng