Matashin Dan Takarar Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheka Daga ADC, Ya Fadi Dalili
- Ɗan takarar mamban majalisar wakilan tarayya a inuwar African Democratic Congress (ADC), Obinna Nwosu, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar
- A wata hira da Legit Hausa, Nwosu ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar ADC ne saboda mutanen mazaɓarsa sun roki ya sake lale
- Ya kuma ƙara da cewa yana buƙatar lokaci kafin ya yanke shawarar jam'iyyar siyasan da zai koma domin buɗe sabon babi
FCT Abuja - Ɗan takarar kujerar mamban majalisar tarayya karƙashin inuwar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ya sauya sheƙa daga jam'iyyar.
Mista Obinna Nwosu ya fafata a zaben mamban majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Ikwuano / Umuahia ta tarayya daga jihar Abiya a zaben 2023.
Ya tabbatar da ficewa daga jam'iyyar ADC a wata sanarwa da ya aike wa Legit Hausa ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023.
Haka nan ya aike da wasiƙar fita daga jam'iyyar ga shugaban ADC na ƙasa, sakatare na kasa, shugaban ADC na jihar Abiya da na ƙaramar hukumar Umuahia ta arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wasiƙar murabus daga kasancewa mamban ADC, Nwosu ya gode wa jam'iyyar bisa damar da ta ba shi na tsayawa takara karkashin inuwarta a babban zaɓen da ya wuce.
Ya kuma tabbatarwa magoya bayansa da masu fatan alheri cewa yana na kan manufarsa ta kokarin gina al'umma na gari.
Wace jam'iyya zai koma?
A tattaunawar da ya yi da Legit Hausa, Nwosu, wanda ya kasance matashin ɗan takarar majalisar tarayya daga Abia, ya ce zai ɗauki lokaci kafin yanke jam'iyyar da zai shiga.
Ya ce zai sanar da matakin da ya ɗauka na gaba a siyasace a lokacin da ya dace. A kalamansa ya ce:
"Na fice daga jam'iyyar a hukumance ranar 29 ga watan Nuwamba, 2023. Game da batun jam'iyyar da zan koma ba sauri nake ba, zan ɗauki lokaci na nemi shawara a lokacin da ya dace."
Dangane da dalilin da ya sa ya fice daga ADC, Mista Nwosu ya ce:
"Bisa la'akari da abin da ya faru a zaben da ya wuce, mutanen mazaɓata suka roƙi na gode wa ADC kana na buɗe sabon shafi a siyasata kuma na saurari kokensu."
Dirama ta faru a zaman NASS
A wani rahoton kuma Wata dirama ta auku a zauren majalisar tarayya gabanin isowar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ranar Laraba.
Wasu sanatoci da basu fahimci yadda ake zaman haɗin guiwa ba, sun wuce zauren majalisar wakilai bisa kuskure.
Asali: Legit.ng