Akwai Matsala: Yan Majalisa 27 Cikin 31 Sun Juya Wa Gwamnan PDP Baya Yayin da Ake Yunkurin Tsige Shi
- Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa mambobi 27 daga cikin 31 na majalisar dokokin jihar Ribas ba su tare da Gwamna Siminalayi Fubara
- Mista Wike, ministan birnin tarayya Abuja ya bayyana haka ne a wata hira ranar Jumu'a kan danbarwar siyasar jihar Ribas
- Rikicin siyasa ya ɓalle a jihar Ribas tun lokacin da yan majalisa suka yi yunkurin tsige Gwamna Fubara a ƙarshen watan Oktoba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ga dukkan alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba a rikicin da ya shiga tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da magabacinsa, Nyesom Wike.
Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja ya ce yan majalisa 27 cikin 31 na majalisar dokokin jihar Ribas sun sa ƙafar wando ɗaya da Gwamna Fubara.
Yadda rikici ya raba majalisa gida biyu
Premium Times ta tattaro cewa jihar Ribas ta wayi gari cikin rigingimun siyasa biyo bayan yunkurun wasu ƴan majalisar jihar na tsige Fubara daga kujerar gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan yunƙuri dai shi ne ya haddasa ƙona wasi sashi na zauren majalisar dokokin jihar a ƙarshe-ƙarshen watan Oktoban da ya gabata.
Tun wannan lokaci dai majalisar dokokin ta dare gida biyu, tsagi ɗaya na goyon bayan Wike yayin da ɗayan tsagin kuma na goyon bayan Gwamna Fubara.
Mafi akasarin yan majalisa ba su tare da Fubara
Da yake hira da ƴan jarida kan rikicin siyasar jihar Ribas a Abuja ranar Jumu'a, Mista Wike ya ƙara zafi kan batun Fubara, yana mai cewa shirin tsige shi bai ƙare ba.
“A kowane hali ka tsinci kanka ka gode wa Allah. Babu wani dan siyasa nagari da zai goyi bayan irin haka amma muka yi shiru, na umarci kowa ya kama bakinsa ya yi shiru."
"Bari in tuna maka, kana da mambobi 31 a Majalisar Dokoki, 27 suna adawa da kai" in ji Mista Wike, yayin da yake magana kan Gwamna Fubara.
A hirar wadda TVC News ta watsa, Ministan Abuja ya yi bayani kan rigimar jihar Ribas ciki harda zargin da ake masa na huro wuta da nufin tsige gwamna mai ci.
Da aka tambaye shi ko yana da hannu a tsige magajinsa, Wike ya amsa da cewa, “Idan suna shirin tsige ka,” yana mai nuni ga magajinsa Fubara, “shin ka kira ni?”
Mista Wike ya ci gaba da cewa: "Alal misali mu ɗauka ni ne na shirya makarkashiyar tsige ka, shin ka kira ni ka ce, 'Yallabai suna so su tsige ni."
Shugaba Tinubu Ya Gana da Ganduje da Gwamnoni Uku
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan Kogi, zababbun gwamnonin jihohin Imo da Kogi tare da shugaban APC na ƙasa
Shugaban ƙasan ya taya su murna, yana mai tuna musu cewa su zama bayi masu yi wa al'umma hidima da gyara jihohinsu
Asali: Legit.ng