Tsige Abba: Tashin Hankali Yayin da APC da NNPP Suka Shirya Gagarumin Abu Rana Ɗaya a Kano
- Jam'iyyar APC ta ce yayin da NNPP ta shirya gagarumar zanga-zanga ranar Asabar a Kano, zata shirya babban rali a wannan rana
- Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin ruɗani kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Abba Kabir Yusuf
- Rabiu Suleiman Bichi, daraktan kamfen Gawuna/Garo, ya ce tun da Kwankwaso ya koma Kano aka samu matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - Tashin hankali na ƙaruwa a jihar Kano yayin da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC da na NNPP suka sanya ranar fitowa zanga-zanga kan tituna.
Dukkan manyan jam'iyyun biyu sun tsaida ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, 2023 domin yin tarukan nuna goyon baya ga gwanayensu bayan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara.
Haka na zuwa ne sakamakon hukuncin kotu wanda ya tsige Abba Kabir Yusuf kuma ya ayyana Nasiru Gawuna na APC a matsayin halastaccen gwamna.
Daraktan kamfen Gawuna/Garo, Rabiu Suleiman Bichi, ya ce jam'iyyar APC za ta shirya gagarumin rali ranar Asabar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC da NNPP sun shirya taro rana ɗaya
Ya bayyana cewa yayin da NNPP za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Asabar, APC ta shirya ralin nuna goyon baya ga Gawuna.
Suleiman Bichi ya faɗi haka ne a hedkwatar APC ta ƙasa, Abuja yayin da ya jagoranci masu ruwa da tsaki da suka ƙunshi ƴan majalisa da tsoffin kwamishinoni.
Bichi ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa masu ruwa da tsakin NNPP sun tsara zanga-zanga ranar Asabar bayan sun gana da jagoransu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya jaddada cewa masu ruwa da tsaki na APC suma za su gudanar da babban taro a Kano a wannan rana, domin nuna goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar.
Zamu bi doka da oda - Bichi
A rahoton Channels tv, yayin da yake amsa tambaya kan yiwuwar barkewar rikici, Bichi ya ce,
"Mu ’yan kasa ne masu bin doka da oda, kuma ba za mu yi wani abu don kawo cikas ga zaman lafiya ba, amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyinmu."
"Abubuwa sun kara dagulewa ne tun da jagoran NNPP, Kwankwaso ya dawo Kano ranar Lahadi kuma ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar."
Gwamma Bello Ya Garkame Lalitar Gwamnatin Kogi
A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ba da umarnin a kulle dukkan asusun gwamnatin jiha da na kananan hukumomi nan take.
Kwamishinan kuɗi na jihar Kogi, Asiwaju Asiru Idris, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023.
Asali: Legit.ng