Akwai Matsala: An Bankaɗo Sabon Shirin NNPP Kan Wasu Ƙusoshin APC a Kano Bayan Tsige Abba

Akwai Matsala: An Bankaɗo Sabon Shirin NNPP Kan Wasu Ƙusoshin APC a Kano Bayan Tsige Abba

  • Ƙura na kara tashi a Kano tun bayan bayyanar kwafin takardar hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Gwamna Abba
  • Jam'iyyar APC ta yi zargin cewa magoya bayan gwamna da NNPP na shirin yadda zasu farmaki jiga-jigan APC ranar Asabar
  • Ta yi kira ga hukumar ƴan sandan Kano da sauran hukumomin tsaro su ankara domin kare zubar da jini da asarar dukiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Har yanzu cece-kuce da ƙura na ci gaba da tashi biyo bayan bayyanar kwafin hukuncin kotun ɗaukaka na tsige Abba Kabir Yusuf mai cike da ruɗani (CTC).

Idan baku manta ba kotun ta tsige Abba daga kujerar gwamnan jihar Kano tare da bayyana Nasir Gawuna na APC a matsayin zababben gwamna.

Kara karanta wannan

Tsige Abba: Tashin hankali yayin da APC da NNPP suka shirya gagarumin abu rana ɗaya a Kano

Jam'iyyar APC ta tona shirin NNPP.
Jam'iyar APC Ta Tona Shirin Magoya Bayan NNPP Bayan Tsige Abba Kabir Yusuf Hoto: OfficialAPC
Asali: Twitter

APC ta fallasa shirin NNPP na tada zaune tsaye

Channels tv ta tattaro cewa masu ruwa da tsaki na APC a jihar Kano sun ja hankali kan wani yunkurin mambobin jam'iyyar NNPP na tada yamutsi da sunan zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darakta janar na kwamitin kamfen Gawuna/Garo, Rabiu Suleiman-Bichi, ya ce magoya bayan NNPP na shirin faramakar kusoshin APC ranar Asabar mai zuwa.

Ya fallasa wannan makirci da yake zargin mambobin NNPP da ƙullawa yayin da yake jawabi ga ƴan jarida a hedkwatar APC da ke birnin tarayya Abuja.

APC ta aike da sako ga hukumar ƴan sanda

Jam’iyyar APC ta yi kira ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano da sauran jami’an tsaro da su kasance a ankare yayin gudanar ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyi.

"Mun samu labari daga majiya mai tushe cewa suna shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ranar Asabar, inda za su tunkari manyan jiga-jigan APC, idan ta yiwu ma su raba su da duniya.”

Kara karanta wannan

Hotuna: Magoya bayan NNPP da Abba sun gamu da babbar matsala yayin da suka fito taro a Kano

"Bisa haka ne muke kira ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano da sauran jami’an tsaro da su zama cikin shiri kuma su ɗauki matakan daƙile lamarin don guje wa rasa rayuka da dukiyoyi."
"Mu mutane ne masu ɗa'a da bin doka, ba zamu yi wani abu da zai ruguza zaman lafiya ba, amma ba zamu yi ƙasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin mu."

- Suleiman-Bichi.

An hana mambobin NNPP taro a Kano

A.wani rahoton na daban Magoya bayan NNPP da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun gamu da cikas yayin da suka fito taron addu'ar neman nasara ranar Alhamis.

Jami'an yan sanda da sibil defens sun hana mambobin jam'iyyar shiga filin da suka shirya taron, bisa dole suka koma gefe ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262